Tsadar Rayuwa: ‘Dan Najeriya ya Kashe N60000 a Fetur Kafin Tankin Mota Ta Cika a Ingila
- Ogbeni Dipo ya bada labarin yadda ya kashe fam £110 kafin ya sha man fetur da zai cika masa tankin mota
- Idan aka yi lissafi a kudin mu na Najeriya, Dr. Ogbeni Dipo ya kashe kimanin N60, 000 ne wajen shan man fetur
- Hakan ya nuna rayuwa ta kara tsada a Birtaniya, a nan kudin nan sun isa albashin matsakaicin jami'i
England - Ogbeni Dipo ya shaidawa Duniya yadda ya kashe makudan kudi saboda ya cika motarsa da man fetur a kasar Ingila.
Malamin jami’ar ya yi magana ne a shafinsa na Twitter, yace sai da ya kashe fam £110.08 kafin ya cika motarsa taf da fetur.
Bayan ya kashe wadannan makudan kudi a gidan mai, Dipo yace sai da ya saye lemu da kayan kwalama domin ya rage zafi.
Idan aka yi lissafi a kudin mu na Najeriya, wadannan kudi sun kai kusan N60, 000, idan har aka yi la'akari da farashin banki.
Mai da araha a Najeriya
A lissafin ‘yan canji kuwa, kudin za su kai N70, 000 a yau. A Najeriya abin da ake saida farashin litar fetur bai wuce N200.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da N10 000, mutum zai iya cika motarsa mai lita 50 a Najeriya idan ya samu gidan mai wanda yake saida lita a farashin doka.
Matashin wanda ya yi yawo a kasashen Turai ya bada wannan labarin ne domin ya nuna yadda rayuwa tayi tsada a Duniya.
Wani mazaunin Birtaniya, ya fadawa Dipo cewa ya saye fetur na £98 a wani gidan man Tesco, amma motarsa ba ta cika ba.
Amma nawa ne albashinka?
Amma Shodeke Temitayo ta fadawa matashin cewa bai kamata yayi lissafin abin da ya kashe ba, kyau ya duba nawa yake samu.
Jaiye Ifeoluwa yace bambancin Najeriya da kasashen ketare shi ne fanfonsu yana da kyau, babu ha’inci a gidajen man fetur a Turai.
Dipo wanda masani ne a harkar Akantanci da kasuwanci da ya yi karatu a Abuja, Coventry da Loughborough bai fadi samunsa ba.
Matashin wanda asalinsa ‘dan Najeriya ne, yana aiki ne a makarantar Nottingham Business School, ya shahara a Twitter da LinkedIn.
Rikicin bizar Atiku
An ji labari cewa rigimar kudi da ake yi tsakanin Legacy Logistics LLC Limited da Alhaji Atiku Abubakar yana iya karewa a gaban kuliya.
Kamfanim yace da aka ga Atiku ya je Amurka kafin zaben 2019, ta hannunsu aka yi takardu, amma har yau kudin bizar da suka yi ba sy fito ba.
Asali: Legit.ng