Damfara ta kare, Alkali Ya Yankewa Mawakin Najeriya Daurin Shekaru 20 a Gidan Yari

Damfara ta kare, Alkali Ya Yankewa Mawakin Najeriya Daurin Shekaru 20 a Gidan Yari

  • Hukumar EFCC ta samu gurfanar da Samuel Onojah da wasu mutane biyu a gaban kotun tarayya a Kwara
  • Alkalin da ya saurari wannan kara a Ilorin, ya zartar da hukuncin dauri a kan wadanda ake tuhuma
  • Lauyan EFCC ya yi shari’a dabam-dabam da wadannan mutane da aka kama kwanaki da zargin damfara

Kwara - Alkali Muhammad Sani na babban kotun tarayya da ke zama a garin Ilorin, jihar Kwara, ya yankewa Samuel Onojah hukuncin dauri.

Mai shari’a Muhammad Sani ya samu Samuel Onojah da laifin da ake tuhumarsa na damfara. EFCC ta fitar da wannan labarin a shafin Twitter.

Hukuncin da Alkalin ya yanke shi ne Onojah da wasu mutum biyu da ake zargi da laifi, za su shafe shekaru 20 a garkame a gidan gyaran hali.

A ranar Litinin, 12 ga watan Satumba 2022, Lauyoyin hukumar EFCC suka gurfanar da Onojah tare da Victor Kadiyamo da wani Jejelowo Segun.

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

Mawaki a gidan kaso

EFCC ta yankin Ilorin ta zargi Onojah wanda mawaki ne da laifin amfani da shafinsa na Instagram wajen damfarar wani da sunan Richard Philips.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin EFCC sun ce Onojah ya yi yunkurin karbar kudi daga wani Erika, kuma ya yi nasarar sace masa £8 wanda hakan ya sabawa dokar kasa.

Yan Yahoo
Yan Yahoo da aka kama Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Kamar yadda EFCC ta bayyana a shafinta, irin wannan danyen aiki ya ci karo da sashe na 22 na dokar damfara ta yanar gizo ta shekarar 2015.

A dalilin wannan, Alkali ya yankewa wanda ake zargi hukuncin daurin shekaru uku a kan laifuffuka biyu da ya aikata ko ya biya tarar N100, 000.

An samu Kadiyamo da Segun da laifi

La’akari da samunsa da laifin aikata sauran zargin da ake yi masa, an yankewa Jejelowo Segun daurin shekaru biyar ko dai ya biya N500, 000.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Shekara 55 Da Ya Lalaba Cikin Dare Ya Saci Plantain Na N4,000 Daga Gonar Wani A Ibadan

Victor Kadiyamo zai yi zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru uku, ko dai ya zabi ya biya N10, 000 da N54,194,680 a kan laifuffukan da ya yi.

Lauyan da ya tsayawa EFCC, Andrew Akoja ya roki mai shari’an ya daure wadanda ake kara. Punch ta kawo wannan rahoto a ranar Larabar nan.

Zaman kashe wando

Kun ji labari Orji Uzor Kalu yana ganin karatun jami’an da ake yi bai isa ba, domin malaman jami’a ba su san abin da suke koyar da dalibai ba.

Tsohon gwamnan na jihar Abia yana da mutum fiye da 13, 000 da ke cin abinci a karkashinsa, ya fadi abin da ke yawan jawo zaman banza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng