Rashin Sallah: Kishin Addini Ya Sa Ya Hakura da Aikin da Yake yi a Kamfanin Mai
- Wani matashi mai suna Abdullahi Sulaiman ya hakura da aikin da yake yi a dalilin hana shi yin sallah kan lokaci
- Abdullahi Sulaiman yace kamfanin da yake aiki a Legas ba su ba shi damar bautawa Ubangijinsa yadda ya kamata
- Saboda haka sai ya rubuta takardar murabus ganin cewa bai dace a sabawa Mahallici saboda ana neman Duniya ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - Mun samu labarin wani matashi wanda ya ajiye aikinsa saboda dalili guda, an hana shi damar da zai rika bautawa Ubangijinsa.
Katsina Post ta rahoto Malam Abdullahi Sulaiman yana mai cewa ya hakura da aikin da yake yi, saboda ya samu damar yin ibada da kyau.
Abdullahi Sulaiman yace ana hana shi yin sallah a kamfanin da yake aiki a garin Legas, ganin halin da ya samu kan shi, sai ya bar aikin.
Rahoton yace wannan Bawan Allah ya fito daga karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, ya kuma tafi Legas da nufin samun na abinci.
Aikin kamfani ya yi tsauri
Malam Sulaiman wanda aka fi sani da Abulali Kankara yana aiki ne lokacin a wani kamfanin mai da ke garin Legas mai suna Nest Oil PLC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da zarar matashin ya tashi zai yi sallah, sai manyansa su hana shi, su fada masa cewa ya dakata tukuna sai ya tashi daga wajen aikin na sa.
Kamar yadda ya fadawa ‘yan jarida a wata hira da aka yi da shi a DCL Hausa, mahukuntansa sun ce ya rika hada sallolinsa idan ya bar ofis.
"Aiki ne nake yi a wani kamfanin mai na Nest oil a nan Legas. Duk lokacin da na nemi su bani dama na je nayi sallah sai su ce a’a…
...wai dole sai dai idan na tashi gaba daya, kana na je na yi. Ni kuma gaskiya ba zan iya hakan ba saboda neman duniya na saba da ubangijina.
Abdullahi Sulaiman
Salloli a kan kari a Legas
Abulali Kankara yace akwai mai irin aikinsa na gadi wanda ya fada masa cewa rabon da ya yi sallar Juma’a tun kafin a dauke shi aiki.
Legit.ng Hausa ta tuntubi malaman addini domin jin ta bakinsu, suka nuna wannan matashi ya yi abin da ya dace a matsayinsa na Musulmi.
Fatawar Abdulaziz Ibn Baaz
Aminu Abdullahi, limami a masallacin ITN Zaria kuma malamin addinin musulunci a jam’ar ABU, ya nakalto mana fatawar Sheikh Abdulaziz Bn Baaz.
Malam Aminu Abdullahi yace da aka tambayi shehin malamin a game da wannan mas’alar yace mutum zai rika yin sallarsa ne gwargwadon ikonsa.
A amsar da malamin ya bada, babu dalilin a jinkirta sallah har sai an tashi daga wurin aiki.
Bn Baaz yace:
“Wanda aka ba tsaron wani wuri ko aka ce ya zauna a wurin ya kula da shi to idan Sallah ta riske shi zai yi ta ne a gwargwadon halinsa da yake ciki, ba zai jinkirta lokacinta ba, gadi ko kula da wani wuri baya hana mutun Sallah, duk lokacin da Sallah ta riske shi zai yi Sallah ne gadi ko kula da wani abu bazai hanashi Sallah ba. Idan wani abu ya faru wanda yake da buqatar hankalin sa to zai je wurin ne koda kuwa zai yanke Sallar."
Majmu'u Fatawa na Imam ibn Baz 29/206
Kamfe a wurin ibada
An ji labari cewa dokar zabe ta shekarar 2022 ba ta yarda wani yayi amfani da coci ko masallatai wajen yakin neman zabe ko a tallata wani.
Festus Okoye yace duk wanda ya yi hakan ya saba dokar kasa, kuma za a iya daure shi a gidan kurkuku ko akalla ya biya tarar N1m zuwa N2m.
Asali: Legit.ng