Gwamnatin El-Rufai ta ji uwar-bari, ta fasa karbar N500,000 na amfani da filin sallar idi

Gwamnatin El-Rufai ta ji uwar-bari, ta fasa karbar N500,000 na amfani da filin sallar idi

  • Da farko Gwamnatin jihar Kaduna ta nemi a biya kudi kafin a iya yin sallah a filin Murtala Muhammad
  • Amma Kaduna State Market Development and Management Company ya yafe biyan kudin daga baya
  • Wannan mataki da Kamfanin ya dauka na karbar N500, 000 a hannun masallaci, ya ba jama’a mamaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Musulmai sun fito su na ta sukar yunkurin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi na karbar kudi kafin ayi amfani da filin Murtala Muhammad Square.

Gwamnatin Kaduna ta nemi a biya N500, 000 kafin Musulmai su iya gudanar da sallar idi na wannan shekara bayan an yi shekaru an saba sallar idi a filin.

Daily Trust ta ce mabiya darikar Tijjaniya da ke masallacin titin Doka a Kaduna sun dade su na yin sallar idinsu a wannan fili da gwamnatin jihar ta mallaka.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Wannan shekara sai aka ji kamfanin kula da kasuwanni na jihar Kaduna ya bukaci mabiya Tijjaniya su biya N500, 000 kafin su iya yin amfani da filin a bana.

Takardar Kaduna State Market Development and Management Company ta jaddada cewa a bana sai an biya kudi domin haka aka yi yarjejeniya da masallacin.

Idan musulmai su na son amfani da filin na Murtala Square domin ayi sallah, an bukaci su biya wannan kudi a asusun kamfanin kafin 6a ga watan Yulin nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin El-Rufai
Gwamna El-Rufai, Sule Kwari, Sani Dattijo da wasu a sallah Hoto: govkaduna
Asali: Facebook

Daga baya sai aka samu labari daga jaridar cewa kamfanin ya yafewa masallacin biyan wannan kudi. Wannan rahoto ya zo a gidan watsa labaran nan na BBC.

Sakataren kwamitin filin sallar idin na Murtala Muhammad, Malam Sunusi Surajo ya tabbatar da cewa an aiko masu takarda, kafin daga baya a yafe masu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

“Gaskiya ne an bukaci mu biya N500, 000 kafin amfani da filin idin Murtala Square, amma mun yi magana da wani wakilin gwamnati, sai aka yafe mana.”
“Wakilin gwamnatin ya ce an bada umarni mu yi amfani da filin haka nan, ba tare da biyan kudi ba.”

Gara dai - Sheikh Haliru Maraya

Da Daily Trust ta zanta da Sheikh Haliru Maraya, ya shaida mata cewa gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta yi dabara da ta canza shawarar karbar kudi.

Shugaban kamfanin da ke kula da kasuwanni, Tamar Nandul ya bada sanarwar yafe biyan kudin. Jamilu Albani ya musanya zargin sanarwar ta fito a makare.

Arafa a Juma'a

Ku na sane cewa Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu da Aminu Daurawa sun yi bayani mai gamsarwa a kan azumin Arafah da zai ci karo da Juma’a.

Rijiyar Lemu ya ce Malamai irinsu Ibn Hajjar, Ibn Qudama da ‘Yan baya-baya irinsu Ibn Baaz sun ce babu laifi don yin azumi a Juma’a idan ya hadu da Arafah

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin jiha ta rushe cocin wani fitaccen faston da ake kai ruwa rana dashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel