Mawakin Duniya zai yi zaman kurkukun shekara 30 saboda lalata da ‘yan mata da yara

Mawakin Duniya zai yi zaman kurkukun shekara 30 saboda lalata da ‘yan mata da yara

  • Alkali ya tabbatar da cewa Robert Sylvester Kelly ya aikata laifuffukan lalata da safarar 'yan mata
  • Tun 2019 aka tsare Mawakin bayan samun shi da laifi da mahukuntan New York da Chicago suka yi
  • Babbar kotu ta gamsu cewa R. Kelly ya yi amfani da shaharar da ya yi, wajen kwanciya da yara

America - Kotu ta yankewa Mawakin kasar Amurka, R. Kelly hukuncin daurin shekara 30 a gidan maza sakamakon kama shi da laifi da Alkali ya yi.

A ranar Laraba 29 ga watan Yuni 2022, BBC ta rahoto cewa Alkali ya samu mawakin da amfani da sunansa, wajen cin zarafin ‘yan mata da 'yan yara.

A Satumban shekarar bara aka yankewa mawakin mai shekara 55 a Duniya hukuncin dauri.

Lauyan Robert Sylvester Kelly ya nuna za su daukaka kara. A wannan lokaci ne mata suka rika fitowa, su na fallasa abin da tauraron ya yi masu.

Kara karanta wannan

Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

Robert Sylvester Kelly ya ci mutuncin mata

Alkalin da ya saurari wannan shari’a, Ann Donnelly ya yanke hukunci cewa Robert Sylvester Kelly ya yi amfani da mata ta munanan hanyoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wajen kwanciya da matan, ya yi sanadiyyar da suka kamu da miyagun cututtukan zamani.

Mawakin Duniya
Tauraro R Kelly a kotu Hoto: www.theguardian.com
Asali: UGC

A zaman kotun, an fallasa yadda Kelly ya yi amfani da damar da ya samu a shekarun baya, ya rika daukar mata da kananan yara domin ayi lalata da su.

Niyyar auren Aaliyah da ba ta kai 18 ba

Har ila yau, an fadawa kotu cewa mawakin ya shirya auren mawakiyar nan da aka yi mai suna Aaliyah a 1994, a lokacin ta na shekara 15 da haihuwa.

Independent ta ce daga baya, Aaliyah ta rasu a shekarar 2001 a wani hadarin jirgi da ya rutsa da ita. Kafin mawakin ya kai ga aurenta, aka lalata alakar su.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Alkali ya yanke hukunci a kan Budurwar da tayi karyar an sace ta

Wannan abin ya yi mani dadi

Jovante Cunningham wanda ta yi aiki da mawakin, ta yi farin cikin yadda kotu ta kama tsohon ubangidanta da laifi, ta ce tayi farin ciki wannan rana.

A cewar Cunningham, ba ta taba tunanin Alkali zai ba wadannan bakaken yara gaskiya ba. Hukuncin Alkalin ya sa mawakiyar alfahari da Amurka.

Banky W zai yi takara a 2023

Kwanakin baya aka samu labari Olubankole Wellington ko kuma Banky W kamar yadda aka fi saninsa ya shiga jam’iyyar PDP domin yin takara a 2023.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi wa mawakin maraba ta musamman. Banky W yana so ya tsaya takarar 'dan majalisa ne a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel