Jami’an tsaro sun cafke wata ‘Zahra’ da ke damfarar Bayin Allah da hotunan tsiraicinsu

Jami’an tsaro sun cafke wata ‘Zahra’ da ke damfarar Bayin Allah da hotunan tsiraicinsu

  • Musa Lurwanu Maje shi ne wanda ya labe da sunan Zahra Mansur, yana tsula tsiya a Facebook
  • ‘Zahra Mansur’ ta kan yaudari mutane su turo hotunan tsiraicinsu, sai tayi barazanar fallasa su
  • A irin haka Musa Lurwanu Maje ya rika karbar kudi daga hannun jama’a, ba tare da an ankara ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Wani matashi mai suna Musa Lurwanu Maje ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda a dalilin damfara da ci da ceto da yake yi a shafin Facebook.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen Kano suka tabbatar da wannan lamari ta bakin Kakakin jami’an, Abdullahi Kiyawa a karshen makon jiya.

Kiyawa a sanarwar da ya fitar a shafukan Facebook ya ce Musa Lurwanu Maje ya amsa laifinsa na yaudarar maza da su turo masu hotunan tsiraicinsu.

Kara karanta wannan

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

Bayan sun turo wadannan hotuna, sai Musa Lurwanu Maje wanda ya fake da sunan Zahra Mansur ya yi masu barazanar fallasa wadannan hotuna.

Da haka sai ya nemi kudi daga hannun wadannan mutane a Facebook da suke tsoron tona masu asiri. Daily Nigerian ta fitar da wannan rahoto jiya da rana.

Zahra Mansur ta kware a yaudara

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan mutumi mai amfani da sunan Zahra Mansur ya kware wajen yaudarar mutane a dandalin Facebook, ba tare da an gane ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zahra Mansur
Zahra Mansur da Musa Lurwanu Maje Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Har ta kai idan wata za ta fitar da bidiyo na kai-tsaye a shafinta na Instagram, Musa Maje ya kan yi kutse, ya shigo da bidiyon a shafin Zahra Mansur a Facebook.

A haka dai wannan matashi da yake karyar shi Budurwa ce da ta karanci ilmin likitanci ya shiga hannu bayan tsawon lokaci yana karbar kudi ta wannan hanya.

Kara karanta wannan

Aure ya kullu: Bidiyoyi da hotuna daga shagalin bikin Lilin Baba da kyakkyawar amaryarsa Ummi Rahab

CP S. Shu’aibu Dikko ya samu korafi

Sanarwar ‘yan sanda ta nuna ana ta samun korafi game da aika-aikar wannan mutumi, don haka Kwamishinan Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya sa ayi bincike.

Jami’in da ya jagoranci cafke wannan mutumi mai shekara 26 shi ne SP Shehu Dahiru. An gano cewa Maje yana zaune ne a cikin garin Sumaila da ke jihar Kano.

‘Yan Sanda sun ce an same shi da wayar zamani ta Redmi Note 11 Pro ta kimanin N200, 000 da kudi har N70, 000 a hannunsa da hotunan tsiraicin wasu mutane.

Kwallon kafa

A baya an ji labari Hukumar FIFA ta amince a buga wasannin gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026 a wasu Birane 16 da ke Amurka, Kanada da kasar Mexico.

‘Yan wasan kwallon kafa za su rika yawo daga Atlanta, Dallas, Guadalajara, Mexico City, Miami, zuwa Biranen Toronto da Vancouver a gasar World Cup 2026.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da su Peter Obi - Kwankwaso ya tabbatar da shirin taron dangi a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng