Ba za a ba Abduljabbar Kabara lauya a kyauta ba – Lauyoyin jihar Kano sun kawo dalilinsu

Ba za a ba Abduljabbar Kabara lauya a kyauta ba – Lauyoyin jihar Kano sun kawo dalilinsu

  • Abduljabbar Nasiru Kabara ya bukaci a ba shi lauyan da zai kare shi, ba tare da ya biya ko sisi ba
  • An hana Sheikh Abduljabbar Kabara lauyan saboda yana iya samun kudin da ya haura N30, 0000
  • Ganin bai cika sharuda ba sai aka ce za a dauko masa hayar lauyan gwamnati, sai ya ce sam ba ya so

Kano - Daily Trust ta ce shekara daya kenan da fara gurfanar da Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin yin kalamai na batanci ga Manzon Allah (SAW).

Ana sane sau da dama shehin malamin yana korar lauyoyinsa saboda sabanin da yake samu da su a yunkurin da suke yi na kare shi a wajen shari’arsa.

Jaridar ta ce Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi kungiyar lauyoyi ta taimaka masa da wadanda za su tsaya masa a kyauta, ba tare da ya biya ko kobo ba.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ya Yi Digiri a Jami'ar Harvard Ta Birtaniya Ya Bayyana Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu

Amma a ranar Alhamis, shugaban kungiyar na reshen Kano, Barista Mukhtar Labaran Usman, ya fadawa kotu cewa ba za su iya ba malamin lauyansu ba.

Shehi ya na samun kudi?

Mukhtar Usman ya ce Kabara bai cancanci a taimaka masa da lauyan da zai kare shi kyauta ba domin yana karbar abin da ya zarce mafi karancin alashi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A doka, N30, 000 shi ne mafi karancin albashin da ma'aikaci zai iya karba duk wata a Najeriya.

Shi dai malamin addinin ya nuna ba ya yin aikin albashin da kudi za su rika shigo masa a kai-a kai, don haka bai da tsayayyen kudin da yake shigo masa.

Abduljabbar Kabara
Abduljabbar Nasiru Kabara Hoto: Tambari Onwayi Annabi Muhammadu
Asali: Facebook

Ganin halin da ya shiga ne sai jagoran na mabiya darikar Kadiriyya ya bukaci a ba shi lauya da zai yi masa aiki kyauta ba tare da aljihunsa ya yi ciwo ba.

Kara karanta wannan

Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista

Sai dai lauyan gwamnati

Lauyan da ya shigar da kara, Barista Yakubu Abdullahi ya roki Alkali ya ba wanda ake tuhuma aron lauya daga ofishin kwamishinan shari’a na jihar Kano.

Amma malamin ya nuna bai son lauyan gwamnati, yana zargin hukuma da neman ganin bayansa, don haka ya ce ba za a kare shi da kyau a shari’ar ba.

Alkali bai yarda da lauyan gwamnati ba

Shi ma Alkalin, Ibrahim Sarki Yola bai yarda a dauki lauyan gwamnati ba, ya rubutawa wnai lauyan kasuwa, Dalhatu Usman takarda ya kare malamin.

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya daga wannan shari’a, sai 9 ga watan Yuni za a sake yin zama.

Abduljabbar Nasiru Kabara yana tsare

Ku na da labari Gwamnatin jihar Kano ta na zargin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara zai iya jawo tashin hankali a gari da irin karatuttukan da yake yi.

Wannan ya sa tun wancan lokaci aka shigar da karar malamin addinin a gaban kotun shari’a. Hakan ya biyo bayan zaman mukabala da ya yi da malamai.

Kara karanta wannan

Nan da 2026, Gaba daya kudin shigan Najeriya bashi za'a rika biya da su: Asusun Lamunin Duniya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng