Wani Bawan Allah ya maida G-Wagon ta zama gingimari, ta dawo motar dakon itace

Wani Bawan Allah ya maida G-Wagon ta zama gingimari, ta dawo motar dakon itace

  • Bidiyon da aka ga wata G-Wagon ta zama gingimari, ta jawo mutane su na ta surutu a Instagram
  • Motar da mutane da-dama su ke burin samun kudin mallakarta, ta zama abin daukowa wani itace
  • Abin tambayar ita ce mai za sa a koma amfani da mota mai tsada irin wannan, ana dauko tarkace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani bidiyo yana yawo da ya nuna yadda wata mota mai ‘dan karen tsada ta zama abin daukar ita ce.

Kamar yadda mu ka ga wannan bidiyo a dandalin Instagram, wannan mota kirar G- Wagon ta zama gingimari.

Legit.ng ta fara ganin gajeren bidiyon ne a shafin instagblog9ja a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, 2022.

Bidiyon ya nuna an zaftare saman bakar motar, ta yadda ta zama za ta iya daukar tulin kaya a cikinta.

Kara karanta wannan

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

Za a iya ganin cewa an cika G-Wagon din da itace alhali motar sabuwa ce kamar daga ledatta ta fito.

Motar ta zama abin labari a gari ne domin mutane su na ta tofa albakacin bakinsu bayan ganin bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ban mamaki a ce motar da mutane su ke burin su mallaka, ta zama wanda ake cika ta da itace.

G-Wagon
G-Wagon dauke da itace Hoto: @instagblog9ja. Daga: Instagram
Asali: Instagram

G-Wagon sai wane da wane

Dama Hausawa na ce kare da kudinsa, sai a jika masa lahaula. Mai motar zai iya duk abin da ya ga dama.

Kamfanin Marsandi ne suke kera wannan mota ta G-Wagon, kuma ta na da ‘dan karen tsada a kasuwa.

A halin yanzu ana saida G-Wagon din da aka kera a ‘yan shekarun nan tsakanin Naira miliyan 70 zuwa 180.

Mutanen Instagram sun yi magana

Masu bibiyar shafin Instagram sun shiga magana a kan wannan sabon salo da ya ratsa shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

@johnkemphotography ya ce:

"Hahahahahah, abin kayatarwa!”
“Toh sai dai, to sai dai.”

Inji @_alexanderoluchi

@wendy_adamma ya rubuta:

“Kasa ta yi wahala abokina.”
“Ta biya bukata, ko ba ta biya ba?”

Inji @kemz_emma

@obiajumike yake cewa:

“Motar da kyawunta duk da haka.”

Ana kashe-kashe a kasar Ibo

An ji labari masu hannu wajen kashe Okechukwu Okoye sun yi barazanar cigaba da yin ta’adi a Anambra.

Kwanan nan aka datse kan ‘dan majalisar Aguata II, Okechukwu Okoye, kuma ana barazanar hallaka wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel