Na musamman: Fasihin dattijo ya kirkiri risho mai amfani da ruwa maimakon gas ko kalanzir

Na musamman: Fasihin dattijo ya kirkiri risho mai amfani da ruwa maimakon gas ko kalanzir

  • Wani dattijon da ya dauki shekaru yana ba da mamaki ya magantu da legit.ng Hausa kan yadda fasaharsa ke tafiya
  • Ya bayyana yadda ya kirkiri risho mai amfani da ruwa domin girki da sauran nau'ikan yau da kullum na aikace-aikacen gida
  • Hakazalika, ya bayyana wata fasaharsa, inda yace ya kirkiri jirgi mai saukar ungulu, kuma jirgin ya tashi a jihar Gombe

Jihar Gombe - Yayin da ake tsananin bukatar mafita ga tsadar rayuwa a Najeriya, wani dattijo ya jima da samar da sauki a wani bangaren; ta hanyar samar da risho din girki mai amfani da ruwa.

Makwanni kadan da suka gabata ne kafafen sada zumunta suka cika da ta'ajibi ganin wani dattijo yana amfani da ruwa wajen samar da makamashi.

Wannan yasa, Legit.ng Hausa tayi tattaki zuwa inda wannan dattijo yake a jihar Gombe domin jin ta bakinsa da kuma tsare-tsaren da yake yi a nan gaba.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Malam Hadi ya kirkiri risho mai amfani da ruwa
Na musamman: Fasihin dattijo ya kirkiri risho mai amfani da ruwa maimakon gas ko kalanzir
Asali: Original

A tattaunawarsa da wakilinmu, Malam Muhammad Hadi Usman, ya shaida cewa, ya yi wannan aiki ne shekaru uku da suka gabata, don haka ya ma kirkiri abubuwa da dama bayan wannan risho.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da yake yiwa wakilinmu bayani kan yadda ya samar da wuta ta hanyar, Malam Hadi yace:

"Wutan lantarki kanta, idan aka yi dogon bincike ai daga ruwa take, domin kuwa an samu wutar lantarki ne daga walkiya da tsawa ta araduwa da bahaushe yake fada daga sama.
"Misali na farko da zaka fahimta yanzu, idan aka ce damuna ta wuce, amma ai akwai gajimare, to amma me yasa ba a yin walkiya ba a yin tsawa? Saboda ba ruwa a cikinsa."

Ya kara da cewa, duba da wadannan misalai, ya rage wa mutum ya yi amfani da iskar oxygen da ke yawa domin tara dabarun samar da wutar, kamar dai yadda ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Hakazalika, ya ce wannan ba sabon abu ne a wurinsa ba, domin bayan wannan ya yi abubuwa da dama, tun da a cewarsa, risho din ya fi shekara uku da kira.

Game da batun risho mai amfani da ruwa, Malam Hadi ya ce ya zauna sun yi shawari da lauyoyinsa da masu bashi shawari cewa, ba yanzu ne lokacin da ya dace ya sayar da fasahar ba.

Na fara kirkira tun 1971, na kirkiri jirgi mai saukar ungulu, inji Malam Hadi

Da aka tambaye ko yaushe ya fara irin wadannan kirkire, Malam Hadi ya ce, akalla ya shafe shekaru sama da 50 yana kan wannan aiki na kirkirar ababen ban mamaki, inda ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa:

"Fara kirkirar abu na sa kasuwa, kuma mutane su gani su ce sun ji mamaki na fara tun karshen 1971. Domin a 1970 da 1971 ni makanikin besfa ne.
" Ta hanyar gyaran besfa, nayi tunanin nayi abin da wani bai taba yi ba a gyaran besfa da aikin besfa.

Kara karanta wannan

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

"A binciken da nayi na gano zan iya kirkirar jirgi helikofta da injin besfa. Na yi shi kuma ya tashi a karshen 1972."

Sai dai, a jawabansa ya ce bayan tashin jirgin an samu matsala jirgin ya fadi a gidan wani, lamarin da ya jawo masa tsaiko ya dakata da aikin bayan samun sabani da iyalansa.

Daga wannan lokacin, Malam Hadi ya jingine aikin gyaran besfa domin kama wata harkar daban, wacce ita mai cike da ban mamaki ce.

Malam Hadi ya ce ya yawata jihohi da kasashen ketare yana koya wa matasa da dukkan masu sha'awa wannan fasaha, kuma yana ci gaba da yi.

Babban abin da yake kara jan hankalin mutane a cewarsa, shi ne yadda bai taba shiga aji domin karatun ilimin zamani ba, amma ya iya turancin da zai iya bincikar littafan kimiyya da fasaha.

A wani labarin kuma, wani matashi mai hazaka daga jihar Kano mai suna Abubakar Maiwada Danjuma ya hada wata Keke wacce ke iya tuka kanta ta hanyar amfani da hasken rana.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

Wannan matashin dai ya daura hotunan keken da ya samar ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda ya bayyana cewa keken za ta iya tuka kanta da kanta idan har matukinta ya gaji. Ya yi amfani da hanyar kimiyya da fasaha ne ya samar da ita.

Tana kuma amfani ne da hasken rana. Hakazalika, Abubakar ya kara da cewa, matukin Keken zai iya amfani da ita wajen cajin wayar salula da kuma na’urar tafi da gidanka, watau kwamfutar Laptop.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.