Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

  • Wasu ma'aurata sun yi maraba da sabon jariri 'yan sa'o'i kadan bayan matar ta kada kuria ta zabi dan takarar jam'iyyar APGA, Charles Soludo, a zaben gwamnan Anambra
  • Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun sanyawa yaron sunan tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN wanda a halin yanzu yake jagorantar zaben na Anambra
  • Rt. Hon Uche Victor Okafor, kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, ya ziyarci ma'auratan domin ganewa idonsa wannan babban abun farin ciki da ya faru

Misis Ngoesina Mabia, wata matar aure a jihar Anambra, ta haifi da namiji sa'o'i bayan da rahotanni sun ce ta zabi Farfesa Charles Soludo, dan takarar jam'iyyar APGA a zaben gwamnan Anambra.

Kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Pidgin ta ruwaito, matar da mijinta sun sanya wa jaririn da suka haifa sunan Soludo.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasu jami'an INEC sun kauracewa zaben Ihiala a Anambra

An samu karuwa: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta sanyawa dan suna Soludo
Yayin da aka ziyarci gidan matar da ta haihu | Hoto: BBC Pidgin
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Rt. Hon Uche Victor Okafor, ya ziyarci ma'auratan don ganewa idonsa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan Anambra ba.

Duk da cewa Soludo ya samu nasara a kananan hukumomi 18 daga cikin 20 da aka bayyana sakamakonsu, an dakatar da tattara sakamakon zabe saboda ba a yi zabe a karamar hukumar Ihiala ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce sai an gudanar da zabe a Ihiala kafin a bayyana wanda ya lashe zaben, duk da cewa Soludo yana kan gaba da kuri’u sama da 50,000.

Ana ci gaba da gudanar da zaben na Karamar Hukumar Ihiala a a halin yanzu a yammacin ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun hana Sanatan APGA shiga garin

Martanin jama'a

Bolanle Adetiran ya ce:

"Wannan jaririn Farfesa Soludo ne, zai fi Farfesa Soludo girma da yardar Yesu."

Goodluck Othuke ya ce:

"Wannan sabon Soludo zai zama dan siyasa nan gaba. Ina taya iyalan wannan sabon Soludo murna."

Daberechukwu Chiekwe Obijuru ya ce:

"Na hadu da prof a UNN kuma ina son halayensa, a 2016, na haifi yaro na sa masa suna Soludo, bisa abin da nake gani, yaron zai fi prof. Oya prof zo ka dauki yaron mu."

Zaben Anambra: Yadda aka tirsasawa jami'in INEC sanya hannu kan sakamakon bogi

A wani labarin, jami’in da ya kawo sakamakon zaben karamar hukumar Orumba ta Arewa, Dr. Michael Otu, ya ba da mamaki a cibiyar tattara zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Lahadi lokacin da ya yi tir da sakamakon da ya sanya wa hannu.

Yace bai yarda da sakamakon ba, PM News ta ruwaito.

Ya zargi jami’in zaben da ya kamata ya yi aiki da shi da hada baki da wasu mutane wajen murde sakamakon zabe a yankin.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.