Latest
Murtala Ajaka, mai neman kujerar Gwamnan jihar Kogi karkashin inuwar jam'iyyar SDP a zaben 11 ga Nuwamba, ya yi zargin cewa shi ne abin harin da ake son halaka wa.
Wata babbar kotun tarayya da ke Osogbo, jihar Osun ta daure wasu mutane biyar na tsawon shekaru biyar a gidan gyara hali akan laifin yada bidiyon tsiraci da damfara.
Tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan ya nuna goyon bayansa ga Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa yayin da ake daf da gudanar da zabe a jihar.
Wata mata ƴar Najeriya da suka haɗu da mijin da ta aura a soshiyal midiya ta faɗi yadda haduwarsu ta kaya, inda yanzu sun yi aure bayan abun ya fara kamar da wasa.
Yan bindiga sun kai hari yankin Gandu da ke kusa da jami'ar tarayya da ke Lafiya a jihar Nasarawa, sun harbi ɗalibi ɗaya sun tafi da wani ɗan kasuwa zuwa cikin daji.
An ba Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), shawara guda biyu kan abin da zai yi bayan rashin nasara a kotun koli.
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, ya buƙaci Shugaba Tinubu da Kashim Shettima su yi murabus daga muƙamansu.
Ana zargin cewa idan mutum ya je jami’ar Legas da kudinsa, zai iya sayen digiri, za a gayyaci Kwamishina da Shugabannin jami’ar Legas domin gano gaskiyar lamarin.
Za a ji cewa ana sayen kowace Dalar kasar Amurka a kan abin da ya zarce N1, 000 a BDC, ‘yan kwanaki bayan an yi ta murnar tashin da Naira ta yi a Najeriya.
Masu zafi
Samu kari