Latest
Fadar shugaban ƙasa ta fito ta yi magana kan batun siyar da hannun jarin $100m na Atiku Abubakar a kamfanin Intels ga kamfanin Orleal Investment Group.
Gwamnan jihar Kano ya shaidawa tsofaffin ma’aikata cewa shi mai kaunarsu ne. Bayan shekaru 'yan fansho su na jiran hakkokinsu, Abba Kabir Yusuf ya share masu hawaye.
Attajirin dan kasuwa, Abdulsamad Rabiu ya ki karban tayin zabarsa da aka yi domin ya shiga kwamitin kudi da gwamnatin Shugaban kasa Tinubu ta kafa.
Mai martaba Sarkin Kazaure ya raba kuɗin zakkah da hatsi ga mabukata 10,000 waɗanda suka cancanci a baiwa kuɗin Zakkah kamar yadda Mususlunci ya tanada.
Tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PRP a zaben 2023, Salihu Tanko Yakasai ya yi musayar yawu da wata budurwa da ta kira shi da dan midiya a twitter.
Kotun Daukaka Kara ta zartar da hukunce-hukunce kan kararrakin gwamnoni hudu wadanda suka tayar da kura bisa zargin cewa an yi tufka da warwara a cikinsu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA) ga Abba Kabir Yusuf da kuma wani Abdulkadir Muhammad.
Wata kotun majistare da ke Ogba, Ikeja a jihar Legas ta bayar da belin wani yaro da ake zargi da satar keken da bai kai Naira 50,000 ba kan kudi naira miliyan 2.
Wasu mata wadanda ke sana'ar sayar da rake sun bayyana damuwarsa kan karancin riba da rashin wadatar raken a bana. Manomin rake duk dai a Kadunan ya fadi dalili.
Masu zafi
Samu kari