Latest
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Olayemi Cardoso ya bayyana cewa duk duniya aiki guda daya tak ta fi tasa wahala a halin yanzu, ya bayyana hakan ne a Abuja.
A yayin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya, rundunar 'yan sanda ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar kebura wato wayoyin wuta a jihar Legas.
'Yan sanda sun yi nasarar kame wasu tsageru, sun kwato makamai tare da kashe wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma.
Rahotanni da suka fito daga baya-bayan nan sun nuna cewa Murja Kunya, fitaciyyar 'yar Tiktok ta bar gidan gyaran hali na jihar Kano da kotu ta tura ta.
Rikicin cikin gida ya shigo APC bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu. ‘Yan Majalisa 6 sun rubuta wasika zuwa Tinubu a kan rigimar da ta ratsa APC a Ondo.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bukaci sojoji da su kara kaimi wajen kakkabe 'yan ta'adda da 'yan bindiga wadanda suka addabi wasu yankunan jihar.
Hamshakin attajiri kuma shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, ya amince a yi wa ma'aikatan rukunin kamfanoninsa karin kudin albashi da kaso 50%.
Bola Tinubu ya aika sako na musamman domin taya Nasir El-Rufai murnar cika shekara 64. Shugaba Tinubu ya yi wa tsohon gwamnan na Kaduna fatan koshin lafiya.
Wata 'yar Najeriya ta sanya 'yan kasarta alfahari bayan da ta fito a matsayin dalibar da ta fi kowa kwazo a jami'ar City da ke Landan. An bayyana irin aikinta.
Masu zafi
Samu kari