
Latest







Da safiyar yau Talata ce 16 ga watan Janairu kungiyar kwallon kafa ta Roma ta raba gari da kocinta, Jose Mourinho saboda wasu dalilai masu yawa da ya shafi kungiyar.

Manyan masu fada aji daga bangarori daban-daban suna ta isa cibiyar taro ta jami’ar Ibadan, inda ake bikin cikar jigon APC, Cif Akande shekaru 85.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ƙara jinjinawa Bola Ahmed Tinubu, shugaban Najeriya bisa abinda ya kira da ceton tsarin demokuraɗiyya a Najeriya.

Rundunar yan sandan Kano ta ce mutumin nan da mota ta buge bayan ya kwace wayar wata ya rasu. Haruna Kiyawa ya ce mutumin ya rasu a Asibitin Murtala.

Gwamn atin kasar New Jersey ta ce za ta dawowa Najeriya dala miliyan 8.9 da aka ajiye a bankin kasar a zamanin mulkin Jonathan, da aka fitar don sayen makamai.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shiga ganawar gaggawa babu shiri da masu ruwa da tsaki da kuma masu sarautar gargajiya kan matsalar tsaro da ta addabi birnin Abuja.

Sabon bayani da suka fito a binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi a badakalar ma’aikatar harkokin jin kai ya haifar da cece-kuce.

Wasu miyagun yan bindiga sun sake yin awon gaba da daliban jami'a a jihar Katsina, inda suka sace wasu dalibai biyu mata na jami'ar Al-Qalam da ke jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun sace Folorunsho tare da mahaifiyarta da 'yan uwanta uku mako biyu baya. An tsinci gawar ta ne tare da ta Nabeeha.
Masu zafi
Samu kari