Latest
Karamin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya sha alwashin kawo karshen 'yan bindigan da suka addabi yankin Arewa maso Yammaci na Najeriya.
Wasu rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi garambawul a mukaman Ministocinsa saboda yadda wasu daga cikinsu ba su tabuka komai ba.
Mun tattaro bayanan manyan sarakunan Najeriya 7 da suka rigamu gidan gaskiya a cikin watanni 8 na shekarar 2024 da muke ciki. Mutuwar Sarkin Gobir ta girgiza jama'a.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bukaci masu siyasantar da matsalar rashin tsaro a jihar da su daina. Ya ce ko kadan ba za su lamunci hakan ba.
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ja kunnen gwamnonin jam'iyyar PDP kan rikicin siyasar jihar, ya ce kada su sake su tsoma baki.
Tsohon Minista a Najeriya, Sule Lamido ya ce tsohon shugaban kasa bai so Bola Tinubu ko Yemi Osinbajo ba a zaben 2023 inda ya ce ya so Ahmed Lawan ya gaje shi.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa, an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa suna shewa bayan samun iko da motocin sulke na sojoji guda biyu a daji.
An kawo ma’aikatun Najeriya da aka shafe watanni babu Ministoci a mulkin APC. A yanzu jihar Filato ba ta da ko Minista guda a majalisar zartarwa.
A cikin shekaru kusan 40, mutane da-dama sun jagoranci NIA wajen aikin leken asiri. A rahoton nan, an kawo jerin sunayen daukacin shugabannin hukumar NIA a tarihi.
Masu zafi
Samu kari