Latest
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya samu goyon bayan hakimai 40 cikin 65 na jihar. Hakan na nufin cewa mafi rinjayen hakiman Kano sun yi mubayi'a ga sabon sarki.
Mai martaba sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana bara da almajirai ke yi a matsayin babbar matsala a harkar karatun allo a fadin Najeriya.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ta nemi afuwar Nuhu Ribadu kan zarginsa da hannu a rikicin masarautar Kano.
Rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa jami'anta na da hannu a rikicin masarautar Kano. Rundunar ta ce an tura sojojin ne domin hana karya doka da oda.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta gano shirin tayar da tarzoma a jihar da wasu bata gari ke yi. Ta yi gargadin cewa za ta cafke duk masu hannuna shirin.
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano. Nadinta na zuwa kwana biyu bayan karbar mulki.
Tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir, daya daga cikin sarakuna 5 da gwamnatin Kano ta rusa masarautunsu ya ce sun karbi wannan hakan a matsayin kaddara.
Yawanci ana yawan samun matsala tsakanin gwamnoni da kuma sarakuna da ke jiharsu wanda hakan ya ke kawo musu matsaloli a zabukan da ake gudanarwa.
Zanga-zanga ta barke a Gaya da Nasarawa a ranar Lahadin nan kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na maido da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Masu zafi
Samu kari