Halin da Musa Mai Sana'a ke Ciki bayan Cewa an Masa Duka kan Tallata Tinubu

Halin da Musa Mai Sana'a ke Ciki bayan Cewa an Masa Duka kan Tallata Tinubu

  • A kwanakin bayan nan aka rika yada rade radin cewa an yi wa jarumin fim, Musa Mai Sana'a duka kan tallata shugaba Bola Tinubu
  • Dan fim din ya fito ya yi bayani kan hakikanin abin da ya faru da kuma halin da ya ke ciki bayan yada jita-jitar cewa an masa dukan tsiya
  • Ya kuma bayyana dalilan da suka sanya shi cigaba da goyon bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a hirar da aka yi da shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Fitaccen jarumin Kannywood, Musa Abdullahi Mai Sana'a ya yi martani ga jama'a kan zargin cewa an farmake shi kan tallata Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa a siyasa kowa yana da damar ya bayyana ra'ayinsa game da wanda ya ke fatan ya samu nasara a zabe.

Kara karanta wannan

An je gidan malamin Musulunci da zai nemi gwamna za a kashe shi

Musa Mai Sana'a
Musa Mai Sana'a na bayani a wani fim. Hoto: Musa Mai Sana'a Kano TV
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Musa Mai Sana'a ya yi ne a wata hira da aka yi da shi wanda DCL Hausa ta wallafa a Facebook.

Wani hali Musa Mai Sana'a ke ciki?

Da aka tambayi Musa Mai Sana'a ya ko an kai masa hari, ya bayyana cewa babu wanda ya kai masa farmaki saboda Tinubu, kuma yana cikin koshin lafiya.

Duk da cewa ya sanar da yana lafiya, Musa Mai Sana'a ya ce ba zai fitar da bidiyo ya nuna jikin shi domin kowa ya kalle shi ba.

Ya ce:

"Jiki na da fuskata ba za a gani yanzu ba, masoyana su yi hakuri, ba yanzu ba. lafiya ta kalau. fuskata, jikina, kafata duk su yi hakuri ba yau za su gani ba."

Maganar tallata Bola Tinubu

Game da tallata shugaba Bola Tinubu domin samun nasara a zaben 2027, Musa Mai Sana'a ya bayyana cewa kowa yana da ra'ayi a siyasa.

Kara karanta wannan

Bayan haura wata 1 ana yaki, Shugaba Macron ya fada wa Amurka gaskiya kan shirin nukiliyar Iran

Ya kara da cewa tallar Bola Tinubu ba ridda ba ce a Musulunci, kuma ba wanda ya tallata shi bai tabe ba kuma ba za a ce mutum zai shiga wuta ba.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a taro a Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maganar Mai Sana'a kan tsaro

Musa Mai Sana'a ya bayyana cewa shi ma dan kan shi yana shiga gari-gari yana cewa akwai matslar tsaro saboda haka ba za a ce yana boye matsalar ba.

Ya ce babban abin da ya ke kira shi ne a rika sanar da hukuma duk lokacin da aka ga wani abu maras kyau a sanar da hukuma domin daukar mataki.

A karshe ya yi kira ga dukkan jama'a da su rika yi wa juna fatan alheri a kowane lokaci, inda ya kara jaddda cewa yana cikin koshin lafiya.

An yi wa Mai Sana'a rubdugu

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan fim din Hausa sun yi wa jarumi Musa Mai Sana'a raddi bayan ya fito yana kare gwamnatin Bola Tinubu.

Aminu Saira da Bello Muhammad Bello na cikin jaruman da suka fito suka yi magana bayan wani bidiyo da mai Musa Mai Sana'a ya fitar.

Mai Sana'a ya kare salon mulkin shugaba Tinubu ne bayan jarumi Sadiq Sani Sadiq ya caccaki gwamnatin tarayya game da matsalar tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng