Musa Mai Sana'a: Ina nadamar tsinewa kaina a fina-finan da na yi a baya

Musa Mai Sana'a: Ina nadamar tsinewa kaina a fina-finan da na yi a baya

A karon farko, jarumin barkwanci a masana'antar shirya fina finan Hausa (Kannywood), Musa Mai Sana'a, ya yi nadamar tsinewa kansa da ya ke yi a fina finai. Mai Sana'a ya yi nuni da cewa fina finansa na fadakarwa ne.

Musa Mai Sana'a a zantawarsa da BBC Hausa, ya ce yana matukar nadamar tsinewa ko la'antar kansa da yake yi, a cewarsa, hakan na faruwane saboda rashin kwarewa.

A cewar jarumin barkwancin, tsine tsinen ya yi su ne a lokacin da yake bako a masana'antar, amma daga baya ya gano cewa hakan da yake yi ba abu mai kyau bane.

Ya ce: "A lokacin da na fara taka rawa a fina finai, ina yin wasu abubuwa da nake tunanin dai dai ne, amma daga bisani wasu mutane suka ankarar dani kuskuren hakan.

"A lokacin, zaku ga yadda nake zagi da tsinewa kaina, amma daga baya na fahimci cewa yin hakan illa ce a gareni, shi yasa na daina," a cewar mai sana'a.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa Bayern Munich ta lallasa PSG har ta dauki kofin UEFA 2020 - Hansi Flick

Musa Mai Sana'a: Ina nadamar tsinewa kaina a fina-finan da na yi a baya
Musa Mai Sana'a: Ina nadamar tsinewa kaina a fina-finan da na yi a baya
Asali: Twitter

Ya ce "Da farko-farkon fina-finai na na yi ta yin abubuwa wadanda ni a ganina dai-dai ne, amma daga bisani bayan da wasu mutane suka ja hankalina a kan abubuwan musamman zagi ko tsinewa kaina da nake, sai na fahimci cewa lallai yakamata na daina".

Mai Sana'a ya ce a yanzu ya kara fahimtar abubuwa a fina-finan hausa na Kannywood, musamman yanzu da girma ya zo masa.

"Wannan ya sa dole na bar wasu abubuwan, musamman yanzu da na fara tara iyali, akwai abubuwa da yawa da na daina, na girma yanzu."

Jarumin wanda ya kwashe shekaru masu yawa a Kannywood ya ce da yawan mutane na ganin kamar yana wuce gona da iri a fina finansa, amma sam ba haka abun yake ba.

"Ina fina finai ne domin sanya farin ciki da dariya a fuskar jama'a, kuma fina finai na sukan danganci iyaye da 'yayansu."

"Duk wani rawa da na taka a cikin film to na yi ne don fadakarwa, domin wa'azantar da masu irin wannan hali su daina," cewar jarumin,

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel