Adam A Zango Ya Magantu kan Rashin Sa Hotonsa a Dakin Hirar Hadiza Gabon
- Rashin saka hoton Adam A. Zango a dakin hira da Hadiza Gabon ta yi ya haddasa muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta
- Magoya bayan Zango da na Gabon sun yi ta musayar yawu, inda jarumin ya fito ya bayyana ra’ayinsa game da abin da ya faru
- Adam Zango ya ce ba shi da wata gaba da Gabon, yana mai cewa abin da ya faru ya jawo ce-ce-ku-ce ne bisa rashin fahimta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Rikici ya kunno kai a kafafen sada zumunta bayan Hadiza Gabon ta wallafa hotunan jaruman da ta sanya a dakin da take hira da jama’a, ba tare da hoton Adam A. Zango ba.
Wannan lamari ya tayar da kura sosai, musamman tsakanin magoya bayan jaruman biyu, inda aka rika muhawara mai zafi kan rashin saka hoton Zango daga cikin jerin.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Adam A. Zango ya yi a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook yayin wata hira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan watsa hotunan, magoya bayan jarumin suka fara neman jin dalilin hakan, yayin da wasu daga cikin jama’a suka fassara abin a matsayin raini.
Martanin Adam A. Zango kan abin da ya faru
A wata hira da ya yi domin fayyace matsayarsa, Adam A. Zango ya ce yana kallon duk abin da ke faruwa, kuma ba shi da wata gaba ko rashin jituwa da Hadiza Gabon ko magoya bayanta.
Ya ce an shaida masa cewa an fara saka wasu jarumai ne a wannan karon, sannan daga baya za a ƙara saka wasu hotuna.
Jarumin ya ce:
“Ba wanda yake da ikon nuna mata abin da ya kamata ta yi. Wannan ra’ayinta ne, kuma masu kallo ma suna da nasu ra’ayin.”
Ya bayyana cewa duk ce-ce-ku-cen da aka yi ya nuna masa irin soyayyar da yake da ita daga jama’a, har ma ya fara tunanin barin fina-finan Kannywood saboda yadda ake nuna masa hassada a baya.
Sai dai goyon bayan da ya gani daga masoyansa ya ƙara masa ƙarfin gwiwa inda zai cigaba da haskawa a duniyar Kannywood.
Zango ya ce ya sha fama da 'yan hassada
A cewar jarumin, shekaru da dama yana fama da matsaloli a masana’antar Kannywood, musamman game da hassada.
Ya ce:
“Cutar damuwa ta kama ni sama da 50 a rayuwata. Abin da ya hana ni mutuwa shi ne tawakkali saboda ni Musulmi ne.”
Ya zargi wasu ‘yan Kannywood da rashin kare shi duk da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, yana mai cewa abin kunya ne yadda sai yanzu ne ‘yan kallo suka fito fili suna goyon bayansa.
Ya ce a baya idan ya nuna damuwa akan cin zarafin da ake masa, sai a zarge shi da rashin haƙuri ko abu makamancin haka.
Ya kara da cewa duk tsawon shekarun da ya yi a Kannywood bai taba yi wa wani rashin kunya balle a ce saboda haka ne aka gaza kare shi:

Kara karanta wannan
"Akwai abin da ba a karya da shi": Rarara ya fadi dalilin aikin alheri a kauyensu
“Ba wanda zai iya fitowa fili ya ce ya masa rashin kunya.”

Source: Facebook
Maganar Tijjani Gandu game da Maryam Booth
A wani labarin, kun ji cewa mawakin Kwankwasiyya Tijjani Gwandu ya yi bayani game da hotunan da ya dauka da Maryam Booth.
A bayanin da ya yi, mawakin ya tabbatar da cewa ba maganar aure ce ta sanya su suka dauki hotuna tare da jarumar ba.
Mutane sun yi ce-ce-ku-ce ne game da wasu hotunan da mawakin ya dauka da Maryam Booth yana mai cewa zai yi bayani daga baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

