Da Gaske Jarumi Ali Nuhu Ya Rasu? Shugaban NFC Ya Warware Rudanin da Aka Samu
- Jita-jita ta karade shafukan sada zumunta cewa fitaccen jarumin Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu ya rasu
- Legit Hausa ta tuntubi makusantan jarumin wadanda suka karyata labarin, sun tabbatar da cewa Ali Nuhu yana nan da ransa
- Ali Nuhu da kansa ya bayyana cewa kowace shekara ana yada irin jita-jitar, inda ya gargadi jama’a da su rika tantance labarai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A makon da ya gabata ne jita-jita ta karade shafukan sada zumunta, cewa fitaccen jarumin Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu ya rasu.
Akwai daga cikin masu yada jita-jitar da suka dauki abin da zafi, inda suka rika wallafa bidiyon wani mutum a makara, suna cewa Ali Nuhu ne.

Source: Facebook
Jita-jitar Ali Nuhu a shafukan sada zumunta
Wata mai amfani da shafin Facebook, Ifeoma Chigbo, ta wallafa bidiyo a shafinta da ke nuna cewa jarumi Ali Nuhu ya rasu.

Kara karanta wannan
Tsohuwar hadimar Buhari ta rubuta masa wasika a kabari, ta fadi yadda APC ta lalace
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ifeoma ta ce tana fatan ace wannan labari ba gaskiya ba ne, amma daga alama ta gasgata bidiyon da ta yada, inda har ta yi wa jarumin addu'a.
Domin tabbatar da wannan magana, Legit Hausa ta tuntubi wani daga cikin makusantan jarumin, wanda ya karyata jita-jitar nan take.
Makusancin ya ce:
"Karya ce kawai ake yadawa. Maigida na nan da ransa, kuma cikin koshin lafiya. Don Allah mutane su daina yada abin da ba su da tabbas a kai.
"Ita mutuwa ai lokaci ce, idan ta zo babu makawa sai an tafi. Amma babu amfani a yi ta yada jita-jitar mutum alhalin yana raye, Allah ya kyauta."
Ali Nuhu ya warware rudanin da aka samu
Bayan jin ta bakin wannan makusancin, sai Legit Hausa ta tuntubi shugaban hukumar fina-finai ta Najerita (NFC), Ali Nuhu don jin ta bakinsa kai tsaye.
Ali Nuhu ya bayyana cewa bai yi mamaki ko kadan ba da irin wannan jita-jitar da ake yadawa, don kusan kowace shekara sai an samu hakan.

Kara karanta wannan
Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa
Fitaccen jarumin ya ce a kowacce shekara ana samun masu yada jita-jitar cewa wani jarumin fim ya rasu, amma a karshe a gane ba gaskiya ba ne.
Ali Nuhu ya nuna muhimmancin bibiyar kafafen yada labarai domin samun sahihan bayanai game da rasuwar jarumai, la'akari da cewar ana cikin zamani na soshiyal midiya.
"Kusan kowacce shekara sai an yi irin wannan. Kuma a wannan zamanin na soshiyal midiya in dai wani jarumi ya rasu ai dole za a gani a kafafen yada labari."
- Ali Nuhu Muhammad.

Source: Facebook
Abin da wasu jarumai ke cewa
Ali Rabiu Ali da ake kira Daddy, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Ina mamakin mutane yadda suke yada jita jita har da dorawa mutane mutuwa. A satin Nan kullum sai an tambaye ni wai Ali Nuhu ya mutu, bayan muna tare da shi a gurin aikin fim din Gidan Sarauta kashi na 5 a garin GOMBE.
"To wai gaggawar ta me ye ne haka? Duk mai rai mamaci ne ai, idan kun yi hakuri ku masu yada jita jitar watarana kuma ba ku da rai sai abinda kuka wallafa za ku bari. Don Allah mu dinga yada alkhairi. Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe."

Kara karanta wannan
Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa
'Abin da ya sa ban kara aure ba' - Ali Nuhu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya magantu a kan dalilinsa na kin yi wa matarsa, Maimuna kishiya tsawon shekaru.
Shugaban hukumar fina-finan Najeriya, Ali Nuhu da matarsa sun shafe tsawon shekaru sama da 20 tare, kuma suna da 'ya'ya biyu a tsakaninsu.
Ali Nuhu ya bayyana cewa sam auren mace fiye da daya ba ya cikin tsarinsa kuma yana ganin hakan ya fi masu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng