Biki Bidiri: Adam A. Zango Ya Zama Ango, Ya Auri Fitacciyar Jarumar Kannywoodo

Biki Bidiri: Adam A. Zango Ya Zama Ango, Ya Auri Fitacciyar Jarumar Kannywoodo

  • An daura auren fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango da Maimuna Musa wacce aka fi sani da Salamatu a shirin Garwashi
  • Wannan biki na zuwa ne mako daya bayan daura auren Jaruma Rahama Sadau, wanda aka yi ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2025 a Kaduna
  • Tuni dai masoya da abokan sana'ar Adam Zango a Kannywood suka fara tura masa sakon murna tare da fatan Allah Ya ba su zaman lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa, Adam A. Zango, dan asalin jihar Kaduna ya angonce.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood, Maimuna wacce aka fi sani da Salamatu a cikin shirin Garwashi.

Adam A. Zango da Maimuna.
Hoton Adam. A Zango a wurin wani shagalin bikin aure, tare da jaruma Salamatu ta shirin Garwashi Hoto: Fauziyya D. Sulaiman
Asali: Facebook

Furodusan Garwashi kuma mai ba gwamnan Kano shawara, Fauziyya D. Sulaiman ta tabbatar da wannan labari a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi na dan majalisar dokoki a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An daura auren Adam A. Zango

Ta bayyana farin cikinta da wannna aure da aka daura, tana mai addu'ar Allah Ya ba ango da amarya zaman lafiya.

Sai dai Fauziyya D. Sulaiman ba ta bayyana lokaci, wuri da ranar da aka daura auren ba, kuma babu wani bayani daga Zango ko ita kanta amarya har kawo yanzu.

Fauziyya ta ce:

"Daga karshe dai Salamatunmu (Maimuna) ta Garwashi ta aure babban jarumi Adam A Zango, na yi matukar farin ciki da wannan aure, Allah ya basu zaman lafiya."

DW Hausa ta tabbatar da wannan lamari, tana mai cewa, "Jarumar Kannywood Salamatu ´Maimuna' ta cikin shirin Garwashi ta amarce da Adam A Zango."

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Adam Zango ya yi aure ba, jarumin ya auri mata a ciki da wajen Kannywood har bakwai amma duka sun rabu da juna.

Jaruman Kannywood sun taya Zango murna

Kara karanta wannan

An samu rudani a sakamakon zaben akwatun Ministan Tsaron Najeriya, APC ta sha da kyar

Tuni dai abokan sana'arsa a masana'antar Kannywood da masoya suka fara taya Zango murna tare da fatan Allah Ya ba su zaman lafiya.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha ya taya ma'auratan murna a shafinsa na Instagram.

"Ina taya ku murnar aure, Allah Ya sanya alheri, Ya ba ku zaman lafiya, kwanciyar hankali da zuri'a dayyiba," in ji Abba.
Jarumin Kannywood, Adam A. Zango.
Hoton Adam Zango a zaune a cikin daki Hoto: Adam A. Zango
Asali: Facebook

Haka nan kuma Sarki Ali Nuhu ya bi sahu wajen taya Adam A. Zango murnar auren da ya yi, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, "Allah Ya sanya alheri ango."

A bangaren masoya kuma, wani mai suna Ibrahim Bala ya ce:

"Masha Allah, ina taya ka murna jarumi na, Ubangiji Allah ya bada zaman lafia Ameen."

Bashir Mohammed ya ce:

"Allah Ya basu zaman lfy, tare da zuri'a dayyaba, Amin."

Rahama Sadau ta yi aure a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa an daura auren fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau a masallacin unguwar Rimi a Kaduna.

Kara karanta wannan

Kannywood: Rahama Sadau da jarumai mata 11 da suka yi aure daga 2022 zuwa 2025

Wannan aure ba tare da sanarwa ba ya ja hankalin masoyan jarumar a kafafen aada zumunta, inda aka rika wa'lafa hotunanta tare da fatan alheri.

Da uwanta, Abba Sadau ya tabbatar da daura auren, yana mai cewa hakan na daya daga cikin burin mahaifinsu, Ibrahim Sadau, wanda Allah ya yiwa rasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel