Jarumar Fim, Ummi Nuhu Ta Fadi Yadda Ta Nemi a Yanke Mata Kafa bayan Karaya 4
- Tsohuwar jarumar finafinan Kannywood, Ummi Nuhu, ta bayyana halin da ta shiga bayan ta ja da baya da fim saboda rashin lafiya
- Ummi ta ce hadari da ta yi ne ya jefa ta cikin mawuyacin hali da har ake tunanin a yanke mata kafa amma likita ya ki yarda
- Ta ce da za ta iya komawa baya, da ta sauya wasu abubuwa da suka faru, ta kuma ce ba ta so ko maƙiyinta ya shiga irin halin da ta shiga
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sake bayyanar tauraruwar finafinan Hausa, Ummi Nuhu, ya sake janyo ce-ce-ku-ce game da kalubalen da wasu fitattun 'yan fim ke fuskanta.
Ummi da ta shahara sosai a Kannywood a shekarun baya, ta bayyana cewa hadarin mota da ta yi ne ya janyo ta janye wa daga harkar a shekarun da suka gabata.

Kara karanta wannan
'Za a rataye shi': Kotu ta yanke wa malamin Musulunci hukuncin kisa a jihar Kwara

Source: Twitter
A cikin hirarta da BBC Hausa, ta bayyana wasu abubuwa masu taɓa zuciya da shawarwari ga matasa 'yan fim, musamman mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadarin da ya janye Ummi Nuhu daga fim
Ummi Nuhu ta bayyana cewa ta yi hadari ne a lokacin da take cikin kololuwar farin jini, inda ta samu karaya hudu a jikinta.
Ta ce akwai lokacin da har tana tunanin dole sai an yanke kafarta, amma wani likita ya hana ayi hakan.
“Na ce a yanke kafar amma likita ya ce a’a. Tun daga lokacin ne aka daina ganina a harkar fim,”
Inji ta
Ta kara da cewa duk da cewa tana da hali a lokacin da ta fara ciwo, daga baya abubuwa suka fara ja baya saboda abin hannunta sun fara karewa.
Ummi ba ta so wani ya shiga irin halinta
Ummi ta bayyana cewa da za ta samu damar komawa baya ta gyara wasu abubuwa, kuma ba ta so maƙiyinta ya shiga irin halin da ta shiga ba.
“Ban so ma makiyina ya shiga irin halin da na shiga. Yanzu na bar wa Allah zabi, komai da ya zaba min zai yarda,”
- Inji jarumar.
Ta nuna cewa ba ta da wata ƙorafi game da rayuwa kuma ta yadda da duk wani hukunci daga wurin Ubangiji SWT.
Ummi Nuhu tana fatan yin aure
Game da aure kuwa, Ummi ta bayyana cewa akwai lokacin da ake so a aure ta, ita ma tana da burin aure, amma lamarin ya gagara.
Ta ce tana fatan Allah SWT ya bata miji na gari kafin ta mutu, amma idan hakan bai faru ba, ta yadda da ƙaddarar Allah.

Source: Youtube
Baya ga haka, Ummi Nuhu ta shawarci mata da ke cikin harkar fim su rika yin kasuwanci domin lokacinsu zai wuce kamar yadda nata ya wuce.
Ummi Nuhu ta rusa kuka ana hira
A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Nuhu ta yi hira da jaruma Hadiza Gabon.
Jarumar ta bayyana cewa ta shiga mummunan yana yi bayan an daina sanya ta a fina-finai saboda zamaninta ya wuce.
Hirar jarumar ya dauki hankali sosai, musamman a Arewacin Najeriya bayan Ummi Nuhu ta rusa kuka ana tsaka da mata tambayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
