Ali Nuhu Ya Sanar da Rasuwar Fitaccen Jarumin Kannywood, Baba Karkuzu

Ali Nuhu Ya Sanar da Rasuwar Fitaccen Jarumin Kannywood, Baba Karkuzu

  • Shahararren ɗan wasan kwaikwayo, Malam Abdul Kano wanda aka fi sani da Baba Karkuzu, ya rasu a ranar Talata, 25 ga Maris, 2025
  • Rahotanni sun nuna cewa za a yi jana'izarsa a ranar Laraba, 26 ga Maris da safe a gidansa da ke layin Haruna Hadeja a garin Jos, Jihar Filato
  • Wani dattijo a jihar Gombe, Malam Adamu Awak ya bayyanawa Legit Hausa yadda ya yi alhinin rasuwar tsohon jarumin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Fitaccen ɗan wasan kwaikwayo na masana’antar Kannywood, Malam Abdul Kano da aka fi sani da Baba Karkuzu, ya rasu ya na da shekaru masu yawa a duniya.

Marigayin ya kasance daga cikin jaruman da suka taka rawar gani a fina-finan Hausa, ya yi fice wajen kwaikwayon barkwanci da darussan rayuwa.

Kara karanta wannan

Hawan sarakuna 2: Yadda jama'a za su tunkari bukukuwan Sallah a jihar Kano

Karkuzu
Dan wasan Kannywood, Baba Karkuzu ya rasu. Hoto: Abdool Gaya
Asali: Facebook

Babban jarumi a Kannywood, Ali Nuhu Muhammad ne ya fitar da sanarwa kan rasuwar jarumin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran jaruman Kannywood sun tabbatar da mutuwarsa, inda suka bayyana jimami tare da yi masa addu’ar samun rahama.

Ali Nuhu da Abba El-Mustapha sun yi addu’a

Fitattun jarumai sun kadu da rasuwar Baba Karkuzu wanda hakan ya jawo suka masa addu'o'i domin samun rahamar Allah.

Ali Nuhu
Babban jarumin Kannywood. Hoto: Ali Nuhu Muhammad
Asali: Facebook

Shahararren jarumi Ali Nuhu Muhammad ya yi addu’a da cewa:

"Allah ya ji kan ka da rahama Baba Karkuzu, ameen."

Hakazalika, jarumi Abba El-Mustapha ya bayyana alhininsa a Facebook da cewa:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Allah ya jikansa, ya gafarta masa kurakuransa, ya sa Aljanna ce makomarsa. Idan tamu tazo, Allah ya sa mu cika da kyau da imani."

Karin jajen rasuwar Baba Karkuzu

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

Bayan labarin rasuwar Baba Karkuzu ya karade shafukan sada zumunta, mutane da dama sun bayyana alhini tare da mika ta’aziyya.

Shahararriyar marubuciya kuma mai taimakon al'umma, Fauziyya D. Sulaiman ta rubuta a shafinta na Facebook cewa:

"Baba, lokaci ya yi. Allah ya gafarta maka Baba Karkuzu. Allah ya sa jinyar ta zama kaffara, amin."

Jama’ar Najeriya sun yi ta’aziyyar Baba Karkuzu

Mutane da dama sun mika ta’aziyya ga iyalan mamacin, inda suka bayyana shi a matsayin mutum mai barkwanci da ilimi.

Malamin addini, Khuzaima Isma’ila Idris ya rubuta a Facebook cewa:

"Ina mika ta’aziyya ga iyalan mamatanmu da Allah ya karbi rayuwansu a yau, iyalan Alhaji Karkuzu."

Al’ummar Kannywood da masu sha’awar fina-finan Hausa sun ci gaba da yi masa addu’a, suna fatan Allah ya jikansa da rahama ya kuma sa Aljanna ce makomarsa.

A yau Talata, 26 ga watan Maris za a yi jana'izar Baba Karkuzu a jihar Filato kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Kara karanta wannan

Babban malami ya hango matsala a Kano, an nemi alfarmar sarki kan hawan Sallah

Legit ta tattauna da Adamu Awak

Wani dattijo a jihar Gombe ya zantawa Legit cewa yana fatan Allah ya gafarta wa Baba Karkuzu, ya sanya shi a Aljanna.

"A shekarun baya, mun nishadantu da wasan kwaikwayo da yake yi. Lallai an yi rashi.
"Bana manta irin yadda yake fita a wasa cikin kayatarwa da jan hankali. Allah ya jikansa."

- Adamu Awak

NNPCL zai yi hadaka da 'yan Kannywood

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi hadaka da 'yan wasan Kannywood.

A wani taro da suka gudanar, an hango Adam A Zango, Rahama Sadau cikin wadanda suka halarci taron hadakar da aka shirya a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng