Ali Nuhu Zai Sa Bulala Ya Zane Jarumar Kannywood, Tana Yunkurin Zana 'Tatoo'
- Ali Nuhu ya gargadi Rayya Kwana Casa'in da ta ajiye shawarar zana tattoo, yana mai cewa zai zane ta da bulala idan ta kuskura
- Jaruma Rayya ta yi tambaya kan yadda mutane suke gani idan ta zana tattoo, lamarin da ya jawo 'yan Kannywood suka yi ca
- Ba iya Ali Nuhu ba, abokan sana'a da masoyan jarumar sun nuna rashin kyautuwar hakan, suna neman ta hakura da yin tatun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shugaban hukumar fina finan Najeriya, Ali Nuhu ya shirya sanya bulala ya zane jaruma Surayya Aminu da aka fi sani da Rayya a cikin shirin Kwana Casa'in.
A ranar Laraba, 25 ga Disamba ne jaruma Rayya ta yi wa masoyanta tambaya wadda ta jawo Ali Nuhu ya taka mata burki kan abin da take shirin aikatawa.
Ali Nuhu ya gargadi Rayya kan zana tatoo
A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Rayya Kwana Casa'in ta tambayi masoyanta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shin ya kuke gani idan na zana hoton Tattoo a jiki na?"
Wannan tambayar ta jawo abokan sana'ar jarumar da ma shugabannin masana'antar Kannywood yin martani mai kama da gargadi.
Ali Nuhu ya gargadi jarumar da ka da ta kuskura ta zana tatoo a jikinta inda ya ke cewa:
"Ke! Kar ki soma wallahi. Bulalar nan tana nan ban jefar da ita ba."
'Yan Kannywood sun takawa jaruma burki
Ba iya Ali Nuhu ba, 'yan Kannywood da dama sun gargadi jarumar kan wannan yunkuri da take yi, kamar yadda Legit Hausa ta tattaro ra'ayin wasu daga ciki.
Madam__korede:
"Wallahi za ki kara kyau rayyah dan kaniyanki."
Officialzeezango_:
"Kar ki yi gaskiya."
Nasirualikoki1:
"Ki rufa mana asiri."
nazir_danhajiya:
"Zan zane ki har sai kin yi kuka."
Jaruma Rayya ta saki zafafan hotuna
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar wasan Hausa, Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya Kwana Casa'in ta saki zafafan hotuna da suka jawo ce-ce-ku-ce.
Masoyan jarumar sun yi Allah wadai da yadda ta bayyana surar jikinta a hotunan da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar murnar haihuwarta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng