Jarumar Kannywood, Rayya Kwana Casa'in Ta Saki Zafafan Hotuna, Ta Jawo ce ce ku ce

Jarumar Kannywood, Rayya Kwana Casa'in Ta Saki Zafafan Hotuna, Ta Jawo ce ce ku ce

  • Fitacciyar 'yar wasan kwaikwayo, Rayya Kwana Casa'in, ta saki hotuna don murnar zagayowar ranar haihuwarta
  • Adam A Zango ya aika mata da sakon fatan alheri, yana addu’ar Allah SWT ya albarkace ta, ya kuma kara mata daukaka
  • A yayin da wasu suke taya jarumar murna tare da addu’o’i, wasu kuma sun nuna rashin jin dadi kan irin shigar da ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitacciyar jarumar Kannywood, Surayya Aminu wadda aka fi sani da Rayya a shirin Kwana Casa'in, ta saki sababbin zafafan hotuna a soshiyal midiya.

Rayya ta saki hotunan ne a matsayin shaidar murnar zagayowar ranar haihuwarta. Sai dai wadannan hotunan sun jawo ka ce na ce mai zafi a intanet.

Adam A Zango yayi magana yayin da Rayya Kwana Casa'in ke murnar karin shekara.
Jaruma Rayya Kwana Casa'in ta kara shekara, ta saki zafafan hotunan da suka jawo ce ce ku ce. Hoto: rayya_90days
Asali: Instagram

Jaruma Rayya ta saki zafafan hotuna

A safiyar ranar Talata, 17 ga watan Disambar 2024, jaruma Rayya Kwana Casa'in ta wallafa hotunan a shafinta na Instagram.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin zuwan sojojin kasar Faransa Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tare da hotunan, jarumar ta wallafa cewa:

"Ina taya kai na murnar zagayowar ranar haihuwata.
"Alhamdulillah."

A karshen shekarar 2021, Rayya Kwana Casa'in ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa shekarunta 21, wanda ke nufin cewa shekarun jarumar yanzu sun kai 24.

Jaruma Rayya ta ce an haifeta a jihar Legas, amma yanzu ta zama 'yar jihar Kano inda take taka muhimmiyar rawa a shirin Kwana Casa'in na talabijin din Arewa24.

Adam A Zango ya aikawa Rayya sako

Dan wasan Hausa, Adam A Zango, ya wallafa hoton Rayya a shafukansa na soshiyal midiya, yana mai aika sakon kalamai masu ratsa zuciya ga jarumar.

A shafinsa na Facebook, Adam A Zango ya wallafa cewa:

"Allah ya raya ki ya ba ki miji nagari ya kara daukaka ya kara maki lafiya da nisan kwana. Ina addu'ar Allah ya karbi dukkanin addu'o'inki ya kuma cika maki burikanki a wannan rana."

Kara karanta wannan

2027: Jam'iyyar APC ta yi zazzafan martani kan ziyarar Kwankwaso ga Obasanjo

Kalli zafafafan hotunan jaruma Rayya da wata Maryam Ibrahim ta dora a shafinta na Facebook:

Hotunan Rayya sun jawo ce-ce-ku-ce

Hotunan jaruma Rayya sun jawo ka-ce-na-ce a shafukan sada zumunta. Yayin da wasu ke taya jarumar murna, wasu kuma na nuna fushi kan irin shigar da ta yi.

sheikh_isah_alolo:

"Murnar karin shekara gareki. Allah ya albarkaci rayuwar ki @rayya_90days"

hally_drippy_wears:

"Ke yanzu wannan rigar idan yau kika koma ga mahalaccinki za ki so a rika yawo da hoton dinkin da wannan rigar?
"Gaskiya daci gare ta kuma kowa yasan gaskiya sai dai a kita. Allah ya shiryamu."

hamza_dogo_dandago_2:

"Ina taya ki murnar karin shekara kanwata doguwa."

Muhammad Habib Abdullah:

"Kamar ba Musulma ba kuma yar musulmi, ko da ya ke yar Kaduna ce, wannan ita ce wayewa a tunanin su, Allah ya shirye ki da mu baki daya."

omar_hajeerh:

"Murnar karin shekara ga uwar gidan gwamnanmu ta Alfawa."

Kara karanta wannan

An yi rashi a Kannywood: Jarumi Baba Ahmadu na shirin Dadin Kowa ya rasu

Ayuba Muhammad Kumo:

"Ya Allah ka shiryar da mu, ka shiryar da duk wanda ya bata amma kuma shi ya na ganin daidai yake."

mijinyawa001

"Murnar karin shekara Surayya. Akwai tsayayye ko in rsaya?"

Mustapha Ahmad Edress:

"Mutane kuna da matsala, wai komai mutun sai kun ce bai yi daidai ba, wai dole ne sai yayi muku ra’ayinku, ya yi mata addu’a, toh menene laifi ko kuskure a ciki?"

'Dan wasan Hausa, Baba Ahmed ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa daya daga cikin jaruman da ke fitowa a matsayin iyaye a masana'antar Kannywood, Baba Ahmed ya rasu.

Shugaban hukumar tace fina finai da dabi'i na jihar Kano, Abba El-Mustapha ne ya sanar da rasuwar Baba Ahmed a ranar Lahadi, 15 ga watan Disambar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.