Mijin aure nake nema ruwa a jallo - Rayya ta shirin 'Kwana Casa'in'

Mijin aure nake nema ruwa a jallo - Rayya ta shirin 'Kwana Casa'in'

- Fitacciyar matashiyar jaruma a Kannywood, Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya, ta ce a kasuwa take

- Ta bayyana cewa, kofarta bude take ga duk mai kaunarta tsakani da Allah

- A kwanakin baya, Rayya ta bayyana cewa ba zata iya auren Yawale ba, saboda yana da mata kuma bashi da irin kudin da take so

Sananniyar matashiyar jarumar fina-finan Hausa mai suna Surayya Aminu, wacce aka fi sani da Rayya, ta bayyana cewa a kasuwa take don kuwa neman mijin aure take.

Jaruma Rayya ta bayyana cewa, a shirye take ga duk wanda yake so da kaunarta tsakani da Allah zai aureta.

Jarumar ta kara da cewa, shi aure lokaci ne, tana sa ran tayi aure nan ba da dadewa ba cikin ikon Allah.

KU KARANTA: Kalubale na farko dana samu farkon shiga ta Kannywood shine iyayena da suka ki amince mini

Idan ba zaku manta ba, a kwanakin baya da Rayya ta tattauna da Dala FM a kan abokin aikinta Yawale, jarumar ta ce ba zata iya aurenshi ba saboda yana da mata. Hakazalika, Yawale bashi da makuden kudin da zata iya aurenshi, saboda ita dai mai kudi take so.

Amma daga bisani, jaruma Rayya ta sanar da janye wannan kalaman a shafinta na Instagram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel