Saratu Daso, El Muaz da Wasu 'Yan Wasan Kannywood 2 da Suka Rasu a 2024

Saratu Daso, El Muaz da Wasu 'Yan Wasan Kannywood 2 da Suka Rasu a 2024

Masana'antar Kannywood ta gamu da rashe-rashen fitatattun 'yan fim da mawaka tun daga farkon shekarar 2024, har ya zuwa yanzu da ta ke karewa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siya

Jihar Kano - Shekarar 2024 da ke shirin karewa a cikin kwanaki 14 ba ta yi wa masana'antar Kannywood dadi ba, biyo bayan rasa jaruman da su ka dade su na bayar da gudunmawa a harkar fim.

Jarumai
An rasa fitattun jaruman Kannywood a 2024 Hoto: Hajiya Saratu Gidado/Mr Abba Dan Ilu/Suleman_Alaka
Asali: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin jaruman Kannywood da su ka rasa rayukansu a cikin shekarar 2024 da ake bankwana da ita, farawa da fitacciyar jaruma a masana'antar fim, Saratu Gidado.

1. Tsohuwar tauraruwar Kannywood, Daso ta rasu

An wayi garin Talata, 9 Afrilu, 2024 da mummunan labari da ya kidama wasu daga cikin 'yan Kannywood, musamman wadanda su ka dade a masana'antar.

Kara karanta wannan

CBN ya kayyade kudin da 'yan Najeriya za su rika cirewa daga masu POS

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TRT Afrika ta ruwaito cewa Saratu Gidado ta koma ga mahaliccinta ta na da shekaru 56 haihuwa da safiyar ranar.

Rahotanni sun bayyana cewa Hajiya Saratu Gidado ta rasu bayan ta kammala sahur, sannan ta koma bacci domin ta huta kafin gari ya waye.

Manyan jaruman Kannywood, irinsu Hamza El Mustapha, shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta Kano sun bayyana kaduwa da rasuwar jarumar.

Kafin komawarta ga Allah SWT, Hajiya Saratu Gidado ta shafe akalla shekaru 18 tauraruwarta na haskawa, inda ta bayar da gudunmawa a matakai da dama.

2. Jarumi Suleiman alaka ya kwanta dama

Masana'antar Kannywood ta yi babban rashi a watan Yuli bayan daya daga cikin shararrun jarumanta, Suleiman Alaka ya riga mu gidan gaskiya.

Darakta kuma tauraro a masana'antar da ake ji da ita, Al-Amin Ciroma ne ya tabbatar da rasuwar alaka a ranar Litinin, 22 Yuli, 2024, lamarin da ya kara dagula Kannywood.

Kara karanta wannan

Manyan sarakunan Arewa da suka fuskanci kalubale daga gwamnoni a 2024

3. Fitaccen mawakin Kannywood ya rasu

BBC hausa ta ruwaito rasuwar fitaccen mawakin Kannywood, El-Mu’az Muhammad Birniwa, dan asalin Jigawa lokacin da ya kammala buga wasan kwallon kafa.

Fitaccen dan wasa a masana'antar Kannywood, Abdul M Shareef, shi ne ya tabbatar da rasuwar mawakin a ranar 5 Disamba, 2024 wanda ya kara jefa masana'antar a cikin jimami.

Da yawa daga cikin jaruman Kannywood sun rika mika ta'aziyyarsu ta shafukan sada zumunta, kafin daga baya a yi wa mamacin sutura kamar yadda Musulunci ya tanada.

4. An kuma rashin tauraron Kannywood

Kwanaki kadan bayan rasuwar El Mu'az ne kuma Kannywood ta sake tsintar kanta a wani hali na alhini a ranar 16 Disamba, 2024.

Wannan ya biyo bayan rashin fitaccen jarumi da ke haskawa a shirin Dadin Kowa na Arewa24, Baba Ahmadu, wanda aka fi sani da hedimasta.

Rasuwar dattijon dan Kannywood din na zuwa akalla kwanaki 11 da rasuwar fitaccen mawaki, El'Mu'az Muhammad Birniwa.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta fara fitar da fetur zuwa kasashen Afrika 4

Shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta Kano, Abba El Mustapha da ya fitar da sanarwar rashin, ya yi addu'ar Allah ya kai rahama ga jarumin.

Rasuwar 'dan Kannywood ta tayar da kura

A baya, kun ji cewa rasuwar jarumi a Kannywood, El-Mu’az Muhammad Birniwa ta bar baya da kura bayan wasu daga cikin jaruman masana'antar su ka shirya casu kwanaki da mutuwar.

Lamarin ya hassala mutanen Kannywood, inda daya daga cikin manya a cikin masana'antar kuma darakta, Nura Ali Koki ya bayyana rashin dacewar hada irin wannan gangami da rasuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.