Nura M Inuwa Ya Samu Cigaba, Za a Fara Nazarin Wakokinsa a Jami'ar Najeriya
- Jami'ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, jihar Jigawa ta amince dalibai su rubuta kundi a kan wakokin mawaki Nura M Inuwa
- Nura M Inuwa ya bayyana wannan babban ci gaba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi wadda ta jawo martanin jama'a
- Dalibin da zai rubuta kundin zai yi nazari kan wakoki biyar, ciki har da “Hindu” da “Duhun Daji," a cewar sanarwar mawakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Burin kowane mawaki shi ne ya zama abin kwaikwayo ga na baya da shi, musamman ganin cewa waka wata bangare ce ta adabi.
A wannan bagire, Nura M Inuwa ya samu babban ci gaba, inda jami'ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, jihar Jigawa ta amince a yi nazarin wakokinsa.
A wata sanarwa da Nura M Inuwa ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi, mawakin ya ce jami'ar SLU ta amincewa wani dalibi ya yi nazarin wakokinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi nazarin wakokin Nura M Inuwa
A cikin sanarwar da ya fitar, mawaki Nura M Inuwa ya dora hoton sakon da dalibin jami'ar ya aiko kamar haka:
"Assalamu Alaikum.
"Sashen Hausa na jami'ar Sule Lamido, Kafin Hausa sun ba ni izinin rubuta kundi a kan wakokin Nura M Inuwa wadanda suke dauke da kalmomi ko jimlolin jarumta a ciki.
"Kamar dai a wakar Hindu.
"Ina bukatar taimakonku domin rubuta wannan kundi na cikar kammala digirin farko a sashen nazarin harshen Hausa da al'adu."
Wakoki 5 da za a yi nazarinsu
Duk da cewa, mawakin bai bayyana sunan dalibin da ya aika masa da wannan sako ba, amma dai ya wallafa wasu wakoki biyar da ake kyautata zaton a kansu za a yi nazarin.
Ga wakokin kamar haka:
- Hindu
- Garkami
- Duhun Daji
- Da Ransu
- Bakin Alkami
Sani Danja ya samu mukami a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen jarumi kuma mawaki a Kannywood, Sani Musa Danja ya samu mukami a gwamnatin Kano a karkashin Abba Yusuf.
A ranar Lahadi, 15 ga watan Disambar 2024, Gwamna Abba Yusuf ya amince da nadin Sani Danja a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan matasa da wasanni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng