Jerin wasu zafafan wakokin Hausa 10 da suka burge jama’a a cikin shekarar 2019
Al’amarin mawaka masu rera wakokin Hausa musamman wadanda suke danganta kawunansu da masana’antar Kannywood na samun tagomashi sakamakon suna buga wakoki na gani na fada dake kayatar da masu sauraro.
Jaridar BBC Hausa ta ruwaito masanin wakokin Hausa, Ibrahim Sheme da Abba Muhammad ne suka gudanar da wani bincike a kan fitattun wakokin da suka yi fice, suka mamaye zukatan masu sauraro, inda suka zakulo guda 10 da suke ganin sun ciri tuta a tsakanin sa’a.
KU KARANTA: Yadda Dasuki ya yi amfani da Sojojin haya daga kasashen wajen murkushe Boko Haram
Masanan sun bayyana cewa tantance fitattun wakoki 10 ba a cikin dimbin wakokin da mawakan zamani suka fitar a bana ba karamin aiki bane, toh amma daga cikin hanyoyin da suka bi akwai bibiyar gidan rediyon FM da talabijin masu sayar da wakoki, ta haka suka tance, suka tantance zafafan guda 10.
Wadannan zafafa 10 sun hada da:
- Hafeez: Umar M Sharif
- Hafeez: Nura M Inuwa
- Kar ki manta da ni: Abdul D One
- So na Amana: Garzali Miko
- Na yi Sa’a: Hamisu Breaker Dorayi
- Abba Gida Gida Abba: Tijjani Gandu
- Baban Abba Ganduje: Dauda Kahutu Rarara
- Sabada: Umar M Shareef da Korede Bello
- Yaran North Side Cypher 2019: DJ Ab, Teeswag, Lil Prince, Jigsaw
- Tsaya: Lilin Baba da Umar M Shariff
Bincike ya nuna baya ga wakokin Abba Gida Gida Abba na Tijjani Gandu da Baban Abba Ganduje na Dauda Kahutu Rarara babu wata wakar siyasa a cikin jerin fitattun wakokin guda 10.
Hakazalika duk da cewa wakokin kishiyoyin juna ne, sun yi tasiri sosai siyasar a shekarar 2019, a yanzu haka a Kano da Injiniya Abba Kabir Yusuf dan takarar gwamnan PDP a jahar Kano sunansa ya bace, sai dai Abba Gida Gida.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng