An Yi Rashi a Kannywood: Jarumi Baba Ahmadu na Shirin Dadin Kowa Ya Rasu

An Yi Rashi a Kannywood: Jarumi Baba Ahmadu na Shirin Dadin Kowa Ya Rasu

  • Masana'antar Kannywood ta rasa jarumi Baba Ahmadu, wanda aka fi sani da Hedimasta a shirin Dadin Kowa mai dogon zango
  • Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha, ya sanar da rasuwar Baba Ahmadu tare da mika sakon ta'aziyyarsa
  • Jarumai da 'yan Kannywood sun yi ta’aziyya, suna bayyana Baba Ahmadu a matsayin jarumin da ya san mutuncin aikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Yayin da ake ta bukukuwan biki da taya jarumi Sani Danja murnar samun aiki a gwamnatin Abba, masana'antar Kannywood ta kuma shiga jimami.

A ranar yammacin Lahadi, aka sanar da rasuwar Baba Ahmadu, wanda aka fi sani da 'Hedimasta' a shirin 'Dadin Kowa' na tashar Arewa24.

Jaruman Kannywood sun yi magana yayin da jarumi Baba Ahmadu na shirin Dadin Kowa ya rasu
Allah ya yiwa Baba Ahmadu na shirin Dadin Kowa rasuwa. Hoto: abbaelmustapha1
Asali: Instagram

Jarumin Kannywood Baba Ahmadu ya rasu

Shugaban hukumar tace fina finai da dab'i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha ne ya sanar da rasuwar Baba Ahmadu a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Atiku ya jajantawa ɗansa kan babban rashin da ya yi, ya ba shi hakuri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar El-Mustapha ta ce:

"Allah ya yi wa Baba Ahmadu, wanda aka fi sani da hedimasta a shirin Dadin Kowa rasuwa.
Muna addu’ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa kurakuransa, ya sa Aljannah madaukakiya ce makomarsa. Idan ta mu ta zo kuma Allah ya sa mu cıka da kyau da imani."

Jarumai sun yi ta'aziyyar rasuwar Baba

Legit Hausa ta tattaro sakonnin ta'aziyya da jarumai da 'yan Kannywood suka aika na rasuwar jarumi Baba Ahmadu:

usmanmuazu20:

"Allah ya jikan Baba Ahmad, daya daga cikin masu fitowa a iyaye a Kannywood, Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareka Baba."

haleemaatete:

"Allah Akbar. Allah ya jikansa da rahama."

sadiqmafia:

"Duk da tsufan shi ya na daraja lokaci da mutunta mutane da kuma girmama sana'arsa. Allah ya gafarta maka Baba Ahmed. Ga godiyan Allah a ko da yaushe, duk inda ku ka hadu sai ya ba ka shawara a kan iyali."

Kara karanta wannan

Kano ta cika ta batse: An daura auren diyar babbar jarumar Kannywood, Asma'u Sani

kamalalkali2:

"Allah sarki Baba Ahmed, Allah ya yi masa rahma"

sultan_abdurrazaq_dorayi:

"Allah ya ji kansa."

Allah ya yi wa mawaki El-Muaz rasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar fitaccen mawakin Kannywood, El-Mua'az Muhammad Birniwa ana tsaka da buga kwallon kafa.

An ce marigayi El-Muaz ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ake buga kwallon kafar bikin mawaki Auta Waziri, inda likitoci suka sanar da rasuwarsa a asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.