An Daura Auren Fitaccen Mawakin Kannywood: Ado Gwanja, Hamisu Breaker Sun Halarta
- A ranar Lahadin nan, mawakin Kannywood, Abdul Respect, ya angwance da Hassana Abubakar Bulama a jihar Kano
- Daurin auren da aka yi misalin karfe 11:00 na safe ya samu halartar mawaka da jaruman Kannywood daga sassa daban-daban
- Jarumai mata da maza, ciki har da Momee Gombe, Ado Gwanja, Ali Nuhu, sun halarci bikin, wanda aka gudanar cikin ban sha’awa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Jihar Kano ta sake yin cikar fari a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba yayin da aka daura auren mawakin Kannywood, Abdussamad Adam.
Mawaki Abdussamad, wanda aka fi sani da Abdul Respect ya angwance ne da amaryarsa Hassana Abubakar Bulama a Hotoro Tsamiyar Boka, Layin Makabarta.
Kamar yadda Abdul Respect ya wallafa katin gayyatar auren a shafinsa na Instagram, ya bukaci 'yan uwa da abokan arziki su halarci wannan aure nasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An daura auren mawaki Abdul Respect da misalin karfe 11:00 na safiya, daurin auren da ya samu halartar manyan mawaka da jaruman Kannywood.
Jarumai da mawaka maza a bikin Abdul Respect
Kafin zuwan wannan ranar ta daurin aure, an gudanar da shagulgula na bikin mawaki Abdul Respect, wanda ya samu halartarsu Ado Gwanja da Hamisu Breaker.
Sauran mawakan da suka samu halartar bikin sun hada da Sadiq Saleh, Dan Musa Gombe, Karaminsu Babbansu, Abdul D One da sauransu.
Baya ga mawaka, akwai kuma jarumai da suka halarci bikin, kamar su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Lawan Ahmad Bakori, Yamu Baba, da sauransu.
Jarumai mata sun yiwa mawaki Abdul kara
Ba iya mawaka da jarumai maza ne suka halarci bikin mawaki Abdul Respect ba, akwai tarin jarumai mata da suka yiwa Abdul kara.
An gano cewa jaruma Momee Gombe ce kirjin biki, yayin da manyan jarumai suka halarta ciki har da Minal Ahmed, Khadija Mainumfashi da Bee Safana.
Sauran jarumai mata da aka ce sun halarci bikin Abdul Respect sun hada da Zarah Diamond, Aisha Izzar So, da dai sauransu.
Kalli hotunan bikin mawaki Abdul Respect a kasa, wanda mai shirya fim, Hamza Dogo Dandago ya wallafa a shafinsa na Facebook.
An daura auren diyar jaruma Asma'u Sani
A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumai maza da na masana'antar Kannywood sun halarci bikin diyar jaruma Asma'u Sani da aka gudanar a jihar Kano.
An ce fitattun jarumai mata na da da na yanzu sun halarci wannan biki, inda Daushe Mai Dabaibayi, Baballe Hayatu da Abba El-Mustapha suka halarci daurin auren.
Asali: Legit.ng