Ya Kamata Ka Sani: Manyan Dalilai 4 da Suka Sa Rahama Sadau Take Shirya Fina Finai
- Rahama Sadau ta bayyana cewa shirya fina-finai wata hanya ce ta isar da sako ga al’umma, ba domin neman kudi kawai ba
- Jarumar ta ce fina-finai na tallata kyawawan al’adu tare da ba da damar fahimtar rayuwar al'ummomi daban-daban
- Jim kadan bayan haska fim dinta mai suna 'Mamah' a Saudiya, Rahama ta yi bayanin dalilanta na shirya fina finai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Saudiya - Rahama Sadau fitacciyar jaruma ce da fuskarta ta karade garuruwa da kasashen da ke kallon fina finan Hausa da na Nollywood.
A lokuta da dama, jaruma Rahama Sadau ta na shan suka kan maganganu ko shigar da ta yi, wanda ke sa wasu tambayar, 'meye ribarta na yin fim?'
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Instagram, fitacciyar jarumar ta kawo karshen ce-ce-ku-ce da ake yi, inda ta lissafa dalilanta na shirya fina finai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama za su dauka jarumar tana yin fim ne kawai don neman daukaka da samun kudi, sai dai Raham Sadau ta ce shirin fim ya wuce nan a wajenta.
Dalilan da ya sa Rahama Sadau ke shirya fim
Rahama Sadau ta bayyana cewa fim wata hanya ce da ke ba al'umma damar isar da sakon wata gwagwarmaya da suka sha a rayuwarsu.
Jarumar ta ce ta hanyar fim, mutum kan iya ba da labarin kyawawan al'adunsa wanda zai ja hankalin al'ummar duniya a kansu
"A kololuwar fahimta, shirya fim ya shafi rayuwar ɗan adam ne kacokam,"
- A cewar Rahama Sadau.
Abu na karshe da ya sa jaruma Rahama Sadau shirya fim shi ne samun damar isar da sakon da zai narkar da zuciyar miliyoyin masu kallo.
An haska fim din Rahama a Saudiya
Jarumar ta yi wadannan maganganu ne jim kadan bayan da aka haska fim din da ta shirya mai suna 'Mamah' a birnin Jiddah na kasar Saudiya.
Rahama Sadau ta ce:
"Muna matukar godiya da gagarumin goyon baya da kaunar da kuka nuna wa fim din mu.
"A gaskiya ina jin kamar mafarki ya zama gaskiya, ganin fim din Hausa ya isa ga masu kallo a duniya kuma ya bar tasiri mai dorewa.
"Wannan ci gaban ya tunatar da mu cewa, duk da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu duka masu ba da labari ne, wanda ya dogara ga matsayinmu na 'yan Adam."
Rahama, Falalu Dorayi sun dura Saudiya
Tun da fari, mun ruwaito cewa jaruma Rahama Sadau, mai ba da umarni, Falalu A Dorayi da wasu 'yan Kannywood sun dura birnin Jiddah na kasar Saudiya.
A wata sanarwa da Rahama Sadau ta fitar, ta ce sun isa Saudiya ne domin haska fim din Hausa na farko a sinimar kasar yayin bikin baje kolin fina finai na 'Red Sea'.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng