Tshohuwar Jarumar Kannywood Ta 'Talauce', Ƴan Damfara Sun Yashe Kudin Asusunta

Tshohuwar Jarumar Kannywood Ta 'Talauce', Ƴan Damfara Sun Yashe Kudin Asusunta

  • 'Yan damfara sun yi kutse a asusun bankunan tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isah inda suka kwashe gaba daya kudinta
  • Tsohuwar matar Sani Danja, ta sanarwa duniya halin da take ciki bayan 'yan damfar sun sace duk wani kudi da ta mallaka a banki
  • Mansura Isah ta aika sako ga wadanda ta yi alkawarin za ta ba su tallafi tana mai kokawa kan rashin samun wanda zai taimaka mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isah ta gamu da sharrin 'yan damfarar yanar gizo inda suka yashe asusun bankunanta.

Mansura Isah wanda tsohuwar matar Sani Danja ce ta sanar da duniya halin da take ciki, tana mai cewa "yanzu ta talauce" bayan abin da ya faru.

Mansura Isah ta bayyana halin da take ciki yayin da 'yan damfara suka yashe kudin bankinta
'Yan damfara sun kwashe dukkanin kudin asusun bankin Mansura Isah. Hoto: mansurah_isah
Asali: Instagram

'Yan damfara sun yashe Mansura Isah

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rikita gari da harbi, sun bi gida gida sun dauki mata da yara

A ranar 3 ga watan Disamba, 'yan damfara suka yi kutse a asusun Mansura Isah a bankuna biyu kamar yadda ta sanar a shafinta na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mansura Isah ta ce:

"Ina cikin wani mawuyacin hali.
"Don Allah, a dakatar da wannan abu yanzu. Fiye da wata guda, ina fama da matsaloli masu yawa. Mutane suna tunanin kamar ƙarya nake.
"Ba zan iya biyan kuɗi ba, ba zan iya sayen abinci ba, ba zan iya taimakon iyalina ba. A wancan karon, na hau motar haya, sai da na zo turawa direban kudi na ga asusuna ya koma N0.00.
"Ta yaya zan rayu? Babu wanda zai ba ni bashi ko ya taimake ni da kuɗi."

Kalli wannan wallafar a kasa:

"Na talauce yanzu" - Mansura Isah ta koka

A ranar 9 ga watan Disambar kuma, tsohuwar jarumar ta sake fitar da karin bayani kan halin da take ciki, inda wannan karon ta ce "ta talauce" ba ta da komai a yanzu.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi fatali da kudin fansa, sun fadi dalilin raina Naira miliyan 3

Mansura Isah ta shaidawa duniya cewa:

"Kamar dai yadda na sanar a baya. Yanzu na talauce."

Mai shirya fina finan Hausa a yanzu, ta ba da hakuri ga wadanda suka tura mata lambar asusun banki na neman taimako da wadanda ta ce za ta taimaka ma wa.

Mansura Isah ta ce a yanzu tana kokari ne ta farfado daga wannan ta'asar da barayin suka yi mata tana mai mika lamuranta ga Allah.

Mansura Isah ta ba 'yan Najeriya shawara

Bayan abin da ya faru da ita, Mansura ta ba 'yan Najeriya shawarar yadda za su kare kansu daga 'yan damfar yanar gizo.

"Idan kuna da katin da kuka hada shi da Google ko wata manjahar biyan kudi ta intanet, ku gaggauta soke wannan tsarin. Ku je banki ku nemi a soke duk wani biyan kudi ta yanar gizo.
"Wallah ba su da imani, kana barci, kafin ka tashi da Asuba, an kwashe duka dukiyarka ta ajiya.

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa rawaninku," Sarki Sanusi II ya fadi abin da ke barazana ga sarakai a Kano

Kuma abin takaici da bakin ciki, ba zaka ga alert ba, balle kasan abinda yake tafiya a cikin asusun ka."

- A cewar tsohuwar jarumar.

Mansura Isah ta yi sabon aure

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa, tsohuwar matar mawaki Sani Danja kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isah ta yi sabon aure.

Babbar kawarta kuma jaruma a masana'ar shirya fina finan Hausa, Samira Ahmed ta sanar da labarin auren Mansura kwanaki kadan bayan aurar da 'yar Sani da Mansura.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.