Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Daga taimako Mansura Isah matar Sani Danja ta shiga tsaka mai wuya (Bidiyo)

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Daga taimako Mansura Isah matar Sani Danja ta shiga tsaka mai wuya (Bidiyo)

- Wani bidiyo da tsohuwar jarumar fina-finan Hausa ta yi, ta bayyana irin halin da ta shiga daga kokarin bada taimako

- Mansura ta bayyana cewa tana cikin tsaka mai wuya a halin yanzu, kuma tana neman taimako a wajen duk wanda yake da hali

- Mansura Isa dai ita ce matar jarumi Sani Danja, kuma ta yi kaurin suna wajen taimakawa marayu da marasa galihu a kasar nan, musamman yankin arewa

Wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sadarwa ya bayyana yadda tsohuwar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Mansura Isah, kuma mata a wajen fitaccen jarumin nan kuma mawaki Sani Danja.

An nuna Mansurah Isah tana bayani akan irin halin da ta shiga a lokacin da suka yi kokarin daukar nauyin wata yarinya mai suna Aisha wacce ta kamu da cutar Daji.

Mansurah ta bayyana cewa an kawo yarinyar daga garin Potiskum ne na jihar Yobe, inda aka yi kokarin yi mata aiki akan cutar da ta kamu da ita, ta bayyana cewa sai da aikin yayi nisa aka kai yarinyar har jihar Legas sai Kakar yarinyar ta bayyana cewa sam baza ayi aikin ba bayan an bayyana mata cewa sai an yankewa yarinyar hannu.

KU KARANTA: Bayan shafe lokaci mai tsawo ba aji duriyarta ba, tsohuwar jaruma Farida Jalal ta dawo shirin fim

Bayan sun yi iya kokarin su wajen ganin sun shawo kanta taki, sai suka hakura Kakar ta dauki yarinyar ta koma gida.

To kwatsam kuma yanzu aka kira ake rokarta cewar jikin yarinyar ya dawo, ma'ana suna neman taimakon ta, Mansura ta ce ita yanzu babu abinda za ta iya yi akan yarinyar saboda bata da halin da zata iya daukar nauyinta, domin kuwa mutanen da suka yi kokarin daukar nauyinta sun cire hannunsu akan lamuranta tun a wancan lokacin.

Yanzu dai jarumar tana rokon duk wanda yake da hali akan ya taimaka wajen nemawa yarinyar lafiya.

Ga dai bidiyon bayanin da Mansura ta yi:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng