Kannywood Ta Ciri Tuta: Za a Haska Fim Ɗin Hausa a Ƙasar Saudiya a Karon Farko
- A karon farko a tarihi, za a haska fim ɗin Hausa a wata sinima da ke birnin Jeddah na Saudiya a yau Litinin, 9 ga Disamba
- Rahama Sadau da Abdul Amart ne suka shirya fim ɗin mai “Mamah” kuma za a haska shi a bikin baje kolin fina finai na Red Sea
- A cewar jaruma Rahama Sadau, wannan babbar nasara ce ga masana'antar Kannywood yayin da ake shirin tantance fim din
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Saudiya - Fina finan Hausa na ci gaba da samun karbuwa a duniya, inda a wannan karon, za a haska wani fim din Kannywood a kasar Saudiya.
Wannan shi ne karon farko a tarihi da aka haska fim din Hausa a kasar Saudiya, kuma karon farko da fim din Hausa ya shiga gasar baje-kolin finafinai a kasar.
Za a haska fim din Hausa a Saudiya
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta sanar da wannan labarin mai dadi a shafinta na Instagram, kuma ta ce za a haska fim din ne a yau Litinin, 9 ga Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahama Sadau da Abdul Amart (Mai Kwashewa) ne suka shirya fim ɗin mai suna “Mamah”, kuma za a haska shi a bikin baje-kolin finafinai wanda za a gudanar a birnin Jeddah.
Fim din Mamah ya samu shiga cikin sahun fina finan da za a tantance su a bikin baje kolin fina finan kasa da kasa na Red Sea.
Rahama Sadau ta yi karin bayani
Jaruma Rahama Sadau ta sanar da cewa:
"Wannan babbar nasara ce kasancewar shi ne fim din Hausa na farko da za a haska a irin wannan babban taro.
Yayin da masu shiryawa da jaruman fim din ke murna, nasarar za ta kawo ci gaba ga masana'antar Kannywood baki daya."
Za a haska fim din a dakin sinima na hudu da ke cikin babban dakin taron baje kolin fina finai na Red Sea Culture, da misalin karfe 10 na safiya.
Hotunan da jarumar ta wallafa a shafin sun nuna Falalu A Dorayi, Rahama Sadau da wasu 'yan Kannywood a wajen dakin taron haska fim din.
Fina finai 5 da za ku kalla a Disamba
A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai fina finai biyar da ya kamata ku kalla yayin da ake shirin fara bukukuwan Kirsimeti na shekarar 2024.
A yayin da kuka samu hutu tare da iyalanku, Legit Hausa ta tattaro fina finan Nollywood da za su sanya ku nishadi da debe maku kewa, kamar fim din 'Silent Night.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng