Ci gaba: Za a haska fim din Kannywood a kasar Amurka

Ci gaba: Za a haska fim din Kannywood a kasar Amurka

An shirya tsaf don fara haska fim din Kannywood mai suna Jalil a Atlanta, Amurka ta Arewa. Daya daga cikin manyan jaruman fim din ne kuma sananne a masana'antar ta Kannywood, Yakubu Muhammed ya bayyana hakan ta shafinsa na Intagram.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Intagram, "Fim mai suna Jalil za a haska shi a Atlanta a ranar 22 ga watan Maris da karfe 4 na yamma. Fim din masana'antar Kannywood na farko da za a fara haskawa a Arewacin Amurka."

A yayin tsokaci, mashiryin shirin, Leslie No'less Dawatda ya wallafa karin bayani a kan hakan. Ya bayyana cewa wannan tamkar somin-tabi ne cikin aikin shi a Najeriya, kamar yadda jaridar jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"Ina godiya ga Yakubu Mohammed da Maryam Booth, gaskiya wadannan kwararru ne. Ba zan manta taimakon da Ali Nuhu da Dimbo Atiya suka yi min ba a lokacin daukar fim din."

Ci gaba: Za a haska fim din Kannywood a kasar Amurka
Ci gaba: Za a haska fim din Kannywood a kasar Amurka
Asali: Twitter

Ya ci gaba da cewa, "Ga duk wadanda suka bada gudumawa wajen hada fim din, muna fatan zaku zama bakinmu a yayin haska fim din a Jos, Kaduna da Atlanta. Zamu kafa babban tarihi a Atlanta tunda wannan ne fim din masana'antar Kannywood da za a fara haskawa a can."

DUBA WANNAN: Zuciya: Dattijo mai shekaru 78 ya dawo gida bayan shekaru 26 da samun sabani da matarsa

Fim din, wanda ya fito daga kamfani Noleess Studio wanda kamfanin hada fina-finai ne da ke Atlanta, an yi shi ne don bada labarin nahiyar Afirka da yadda take.

Za a haska fim din ne a Plaza Theatre, 1049 Ponce De Leon Avenue Northeast Atlanta, GA 30306 a Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel