KILAF 2019: Masana'antar Kannywood ta kafa tarihi, an kammala bikin baje kolin fina-finai a Kano

KILAF 2019: Masana'antar Kannywood ta kafa tarihi, an kammala bikin baje kolin fina-finai a Kano

Masana'antar Kannywood ta kafa wani babban tarihi a cikin shekaru kusan 20 da tayi da kafuwa. An kammala bikin baje kolin fina-finan asalin kabilun jihar Kano (KILAF). Manajan daraktan 'Moving Image Limited Kano, Alhaji Abdul-Kareem Mohammed ne ya kirkiro bikin baje kolin a shekarar 2018.

Amma a 2019, makirkirin bikin ne ya shirya kuma yayi masaukin baki. Bikin na wannan shekarar ya bayyana kirkire-kirkiren da zasu habaka masana'antar fina-finan Hausan. An kwatanta bikin wannan shekarar da biki na musamman duba da yadda aka shiryashi. Bikin ya bada damar bayyana al'adun kabilun nahiyar Afirka.

Kamar yadda shugaban alkalan, Dr Nura Ibrahim ya bayyana, alkalan sun samu fina-finai 56 don tantancewa. Ya kara da cewa, alkalan sun yi kwanaki biyar suna aikin tantance fina-finan da suka cancanci karbar lambar yabo a bikin baje kolin.

DUBA WANNAN: Daga zuwa zaman jego, siriki ya dirkawa mahaifiyar matarsa ciki

"Kafin ba labari maki, sai mun dubi ingancinsa, ta yadda aka hada shi da kuma daki-dakin yadda labarin ya kasance. Muna duba yadda aka bada umarni da kuma yadda 'yan wasan suka isar da sakon da ke kunshe a labarin," in ji shi.

An fara bikin wannan shekarar ne da horarwa, bayyanar da al'adu, sai koyawa matasa dabarun wasan kwaikwayo tare da liyafar cin abincin dare inda aka bada lambar yabo ga wasu 'yan wasa da mashirya fina-finai a Bristol Palace Otal dake Kano.

A liyafar cin abincin daren. Alhaji Abdul-Kareem Mohammed ya bayyana makasudin shirya bikin baje kolin. Ya ce, "abun haushi ne a ce mutum na ji na gani ya bar al'adarshi ta gurbace ba tare da wani kwakwaran dalili ba,"

KILAF ta bada lambobin yabo ga 'yan wasa da mashirya fina-finan hausa da suka hada da Ibrahim Mandawari, Rahma Hassan, Ahmed Alkanawy, Nelcon Nel da Yasin Auwal, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng