Birniwa: Bidiyon Karshe na Fitaccen Mawakin Kannywood Kafin Mutuwa ta Dauke Shi
- Jarumai, furodusoshi da darakotoci, mawaka da sauran 'yan Kannywood sun yi matukar girgiza da rasuwar El-Muaz Birniwa
- Jarumi Abdul M Shareef da mai shirya fim, Falalu Dorayi sun tuno da abubuwan da suka faru a daren ranar da El-Muaz zai rasu
- 'Yar wasa Teema Yola ta wallafa wani bidiyo da ake kyautata zaton shi ne bidiyon karshe na El-Muaz Birniwa kafin rasuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Masana'antar shirya fina finan Hausa, da aka fi sani da Kannywood, ta girgiza matuka da samun labarin rasuwar mawaki El-Muaz Birniwa.
Tun daga daren ranar Laraba, har zuwa washe garin yau (Alhamis), babu abin da ake gani a dandalin Kannywood face jimamin rasuwar Birniwa.
A zantawar Legit Hausa da fitaccen jarumin Kannywood, Abdul M Shareef a safiyar Alhamis, ya ce mutuwar mawaki El-Muaz ta jefa kowa a jimami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Muaz ya buga kwallo kafin rasuwarsa
Abdul M Shareef ya ce suna tare da El-Muaz a daren ranar da ya rasu, a wani wurin buga kwallo, inda ake wasan kwallo na bikin mawaki Auta Waziri.
Jarumin ya ce kamar yadda aka saba yin wasan kwallon sada zumunta idan jarumi ko mawaki zai yi aure, haka aka shirya wasan kwallon murnar auren Auta Waziri.
A cewarsa, El-Muaz ya shiga filin wasan, har zuwa wani lokaci da ya ce yana jin jiri, a nan dai ya yanke jiki ya fadi kasa, aka tafi da shi asibiti.
Kamar yadda aka samu labari, a asibiti ne aka tabbatar da rasuwar mawakin a jiya.
Abdul M Shareef ya kara da cewa shi kansa marigayi El'Muaz din yana shirin aurar da wata kanwarsu a wannan makon, ashe da rabon ba da shi za ayi bikin ba.
Falalu Dorayi ya jaddada maganar M. Shareef
Kafar labarai ta TRT Hausa ta fitar da wata tattaunawa da ta yi da Furodusa Falalu Dorayi, wanda ta jaddada abin da Abdul M Shareef ya fada.
A cewar rahoton, Falalu Dorayi ya ce:
“An je ƙwallo irin ta aure ɗin nan wasu ma sun ce ba a gama ta ba sai ya ce jiri na kwasarsa, daga haka sai ya faɗi.
"Aka ɗauke shi aka wuce da shi asibiti a nan Kaduna, to bayan kamar awa guda ne asibitin suka ba da sanarwar cewa Allah Ya yi masa rasuwa."
Rahotanni sun ce fitaccen mawakin ya rasu ne sakamakon bugun zuciya a lokacin da ake buga kwallon murnar bikin abokin sana'arsa, Auta Waziri.
Bidiyon mawaki El-Muaz na karshe
Fitacciyar jarumar Kannywpod, Teema Yola ta wallafa bidiyon da ake kyautata zaton shi ne na karshe na mawaki El-Muaz Birniwa kafin rasuwarsa.
Bidiyon da jaruma Teema Yola ta wallafa a shafinta na Instagram ya nuna El-Muaz a cikin filin wasan kwallon kafa tare da sauran 'yan Kannywood, cike da nishadi.
An ji wacce ke daukar bidiyon tana cewa:
"Ga Kawu El-Muazu."
Kalli bidiyon a kasa:
Fitaccen mawaki, El-Muaz Birniwa ya rasu
Tun da fari, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar fitaccen mawakin siyasa, soyayya da zamantakewa, wanda kuma ya shahara a Kannywood, El-Muaz Birniwa.
An rahoto cewa mawaki El-Muaz Birniwa ya rasu ne jim kadan bayan kai shi wani asibiti a Kaduna lokacin da jiri ya kwashe shi a filin wasan kwallon kafa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng