KAI TSAYE: Nigeria 1-1 Tunisiya (Wasan kwallon sada zumunta)
Najeriya ta fara buga wasan sada zumunta da kasar Tunisiya a filin kwallon Jacques Leman dake Austria ranar Talata, 13 ga Oktoba.
Wannan shine karo na 20 da kasashen biyu zasu kara kuma kowanne ya ci wasannin shida-shiga yayinda akayi kunnen jaki a bakwai.
Wasan farko da Najeriya t
a buga ranar Asabar ta sha kashi hannun kasar Aljeriya da ci daya bai ban haushi.
Okt 13 9:27 Yamma
An tashi wasa 1-1
Sai watan Nuwamba inda za'a fara wasan fiddan gwanin kofin nahiyar Afirka.
Najeriya za ta buga da Sierra Leone
Okt 13 8:29 Yamma
An tafi hutun rabin lokaci
Okt 13 8:03 Yamma
An kifar da Ahmed Musa a 18, an samu fenariti amma Iheanacho ya barar
Okt 13 7:55 Yamma
Kelechi Iheanacho na Najeriya ya zura kwallo daya