Allah ya yiwa shahrarren mawaki, Hassan Wayam, rasuwa
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya yiwa shahrarren mawakin Hausa, Hassan Wayam rasuwa.
Wayan ya rasu ne yana mai shekaru 64 a daren Juma'a a asibiti bayan dogon jinyan da yayi fama da shi, cewar majiyoyi.
Hassan Wayam wanda aka haifa 1956 a kauyen Gwadda dake karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, ya fara waka ne a garin Mayanci sannan ya koma Zariya a 1969, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya shahara a Arewacin Najeriya inda yake waka a taruka.
Wakokinsa mafi shahara sun hada da “Tana Kukan Kurciya”, “Ba Ni Ne Na Fada Ba, Hassan Wayam Ne Ya Fada”, “Kowac Ci Kurciya”, da sauransu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng