Bayan Rahama Sadau, Mahaifiyar Wata Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Kwanta Dama

Bayan Rahama Sadau, Mahaifiyar Wata Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Kwanta Dama

  • Masana'antar Kannywood na jimami bayan rasuwar mahaifiyar jaruma Rukayya Ahmad Aliyu, wanda aka fi sani da Ruky Alim
  • Mai shirya fina-finai, Bashir Maishadda, da 'yar wasa Momee Gombe suka sanar da rasuwar, suna masu addu'ar Allah ya jikanta
  • Abba Gezawa ya bayyana jaruma Ruky Alim a matsayin jaruma mai mutunta kowa, ya roki Allah ya ba iyalan haƙurin rashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Masa'antar shirya fina finan Hausa da aka fi sani da Kannywood ta sake fadawa cikin jimami yayin da mahaifiyar jaruma Rukayya Ahmad Aliyu ta rasu.

Masu kallon fina finan Hausa da wakokinsu sun fi sanin Rukayya Ahmad Aliyu da sunan 'Ruky Alim'.

Bashir Maishadda ya yi magana yayin da mahaifiyar jarumar Kannywood ta rasu
Mahaifiyar jarumar Kannywood Ruky Alim ta rasu. Hoto: @rukkky_alim
Asali: Instagram

Mahaifiyar jaruma Ruky Alim ta rasu

Mai shirya fina finai, Bashir Abubakar Maishadda ya fitar da sanarwar rasuwar mahaifiyar Ruky Alim a shafinsa na Instagram a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Zuwan Tinubu Faris: Najeriya ta kulla yarjejeniyar ma'adanai da Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"InnalilLahi wa'inna iLaihi raji'un. Allah ya yiwa mahaifiyar jaruma Rukayya Ahmad Aliyu rasuwa."

- A cewar sanarwar Maishadda.

Babban mai shirya fina finan, ya yi wa mahaifiyar jarumar addu'ar neman gafara da kuma rokon Allah ya sanya ta a gidan Aljannah.

"Allah ya gafarta mata. Allah ya sa Aljannah makomarta, ameen summa ameen @rukkky_alim."

- Inji mai shirya fina finan.

Momee Gombe ta yi wa Ruky Alim ta'aziyya

A hannu daya, ita ma jaruma Momee Gombe, ta yiwa jaruma Ruky Alim ta'aziyyar wannan rashi da aka yi mata.

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Instagram, Momee Gombe ta ce:

""InnalilLahi wa'inna iLaihi raji'un. Allah ya baki hakurin rashi Rukayya. Allah ya jikan mama, Allah ya sa ta huta."

"Rukayya mutuniyar kirki ce" - Gezawa

Legit Hausa ta tuntubi daya daga cikin 'yan Kannywood, Abba Hassan Gezawa, wanda ya ce mutuwar mahaifiyar Rukayya ta girgiza kowa.

Kara karanta wannan

"Zan magance matsalolin Najeriya," Tinubu ya bayyana shirin da ya yiwa talakawa

Abba Gezawa ya ce jaruma Ruky Alim mutuniyar kirki ce "wacce ke mutunta duk wanda ta hadu da shi a wajen aiki, kuma ba ta da girman kai."

Marubucin fina finan ya yi addu'ar Allah ya jikan mahaifiyar jarumar "ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan rashi da suka yi."

Kakar jaruma Rahama Sadau ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar kakar fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau a makon da ya gabata.

Rahama Sadau ta ce ita da ahalinsu sun shiga cikin tashin hankali na rasuwar kakarsu, wadda ta ce ta ba su gudunmawa daga yarinta har zuwa girmansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.