'Ki Ba Ni Lokacinki': Bidiyon Wakar Abdul D One da Ya Jawo Ce Ce Ku Ce a Soshiyal Midiya

'Ki Ba Ni Lokacinki': Bidiyon Wakar Abdul D One da Ya Jawo Ce Ce Ku Ce a Soshiyal Midiya

  • Mawaki Abdul D One ya saki zazzafan bidiyon wakarsa mai taken 'Kibani Lokacinki' wanda ya jawo mutane suka rika maganganu a kai
  • Wani masoyin mawakin ya ce salon da aka yi amfani da shi wajen rera wakar, da kuma tsarin da aka dauki bidiyon kamar ba a Hausa ba
  • Aisha Najamu ce ta taka rawa a cikin bidiyon wakar wanda masu kallo da dama suka nuna cewa ta yiwa Abdul D One girma a bidiyon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A kwanan nan ne fitaccen mawakin Kannywood, Abdul D One ya saki bidiyon wakarsa mai taken 'Kibani Lokacinki' wadda ya dauke ta tare da Aisha Najamu 'Izzar So.'

Kara karanta wannan

'Ta kone kurmus,' Matashi ya babbaka kakarsa mai shekaru 60 da fetur

Wakar Kibani Lokacinki ta samu karbuwa a wajen masoya sauraro da kuma kallon wakokin Hausa, bayan da aka shirya wakar a wani yanayi da ba a saba gani ba.

Wakar Abdul D One mai taken 'Kibani Lokacinki' ta jawo ce ce ku ce a sohiyal midiya
'Kibani Lokacinki': Bidiyon wakar Abdul D One da ya jawo maganganu. Hoto: official_aisha_izzar_so
Asali: Instagram

Tsarin daukar bidiyon Kibani Lokacinki

A farkon bidiyon wakar an nuna mawaki Abdul D One a matsayin direban jirgin sama, wanda yake kan hanyarsa ta zuwa aiki amma ya hadu da Aisha Najamu a cikin filin jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk wani kokari na yin magana da kyakkyawar bsudurwar ya ci tura yayin da kuma jirginsa ke shirin tashi wanda ya tilasta shi hakura da yin magana da ita ya tafi wajen aikinsa.

Bayan samun nutsuwa, ya yi kokarin neman kyakkyawar budurwar da ya hadu da ita amma ya gaza samunta ko a soshiyal midiya, lamarin da ya jefa shi a damuwa.

Sai dai rana daya kwatsam ya ci karo da ita a wajen cin abinci, inda nan ma taki kula shi. Amma sai ga wata mai kama da ita ta bayyana, kuma ta zo masa da kalaman soyayya.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

Sharhi kan bidiyon wakokin Hausa

A zantawarmu da Abdulaziz Ya'u Shareef ya ce yanzu Abdul M Shareef na daya daga cikin mawakan da ke canja salon bidiyon wakokin Hausa.

Ya'u Shareef ya ce masu taka rawar gani a wajen daukar bidiyon wakoki a Hausa su ne Umar M Shareef, Hamisu Breaker, Sadiq Saleh, Ali Jita da sauransu.

Jarumin mai tasowa ya ce yana kyautata zaton cewa horon da Abdul D One ya samu a wajen Umar M Shareef ya na kara masa tasiri a wakokin da yake yi.

Bidiyon wakar ya jawo ce ce ku ce

Da Legit Hausa ta bibiyo bidiyon wakar da Abdul D One ya dora a shafinsa na YouTube, mun fahimci cewa wakar ta samu karbuwa yayin da ta jawo maganganu daban daban.

@Marketowntv:

"Ya kamata a kara ta biyu domin wakar nan ta ba da citta."

@firdausiabdullahi5387:

"Salon wakar, bidiyon da komai na wannan wakar ya kayar da ni."

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

@AbdullahiAlamin-v7o:

"Aisha Najamu jaruma ce mai nagartar gaske, akwai banbanci tsakanin ta da 'yan bana bakwai."

@muhammadibrahimdass5664:

"Gaskiya wannan bidiyon ya ba da ma'ana, kamar ba a wakar Hausa ba."

@abbadikke:

"Masha Allah. Ina kaunar tsarin da aka dauki bidiyon, ya yi kyau sosai."

@realmatashidon2846:

"Wannan bidiyon ya dauku sosai."

@Bosskidfamouzz:

"Wannan dai ba ta dace da bidiyon ba, ai yarinya za ka nemo."

Kalli bidiyon a kasa:

Mawaki ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin soyayya, zamantakewa da ma siyasa, Ali Isah Jita ya hakura da tafiyar Kwankwasiyyya inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Sauya shekar Ali Jita na zuwa ne yayin da 'yan Kannywood da dama ke korafin yadda shugabannin Kwankwasiyya ke yi masu rikon sakainar kashi a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.