Fitaccen mawakin Kannywood ya tabbatar da soyayyarsa ga shahararrar Jaruma, Gabon

Fitaccen mawakin Kannywood ya tabbatar da soyayyarsa ga shahararrar Jaruma, Gabon

Shahararren mawakin nan Naziru Ahmad, ya bayyana matsayin alakarsa da fitaccen jarumar Kannywood, Hadiza Gabon a cikin wata hira ta musamman da yayi da jaridar Aminiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da aka tambaye shi menene alakarsa da Hadiza Gabon, sai ya kada baki yace tabbas suna soyayy da juna, kuma suna matukar son juna ba wai bane, Naziru bai tsaya nan ba, ya cigaba da cewa:

“Mutum ba zai ce ya yi asara idan yana soyayya da ita ba. Amma a zahirin gaskiya ba a sa ranar aurenmu ba, komai na Allah ne”- Inji shi.

KU KARANTA: Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa: Wani Gwamnan a Najeriya zai fara biyan ma’aikatan jiharsa kudin bacci

Fitaccen mawakin Kannywood ya tabbatar da soyayyarsa ga shahararrar Jaruma, Gabon
Jaruman

Sai dai a yayin tattaunawar, mawakin ya musanta batun da ake yadawa na cewa wai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bashi kyauytar kudi naira miliyan 50 biyo bayan wata waka da yayi masa, inda yace ba gaskiya bane, “Amma b azan bayyana abinda ya bani ba.” Inji shi.

Dayake karin haske game yadda ya tsunduma waka, Naziru ya bayyana cewa ya fara waka ne a shekarar 2002, inda yace zuwa yanzu yana has ashen adadin wakokin da ya rera a tun bayan fara waka gadan gadan sun kai 300.

Daga karshe ya bayyana ma majiyar mu cewar duk a cikin wakokinsa ya fi kaunar wakar ‘Dan Adaln Mubi’ da kuma ‘Sardaunan Dutse’, musamman saboda a cewarsa duk abinda ya fada a cikin wakar ya gansu a zahiri, wasu kuma ya ji su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel