Borno: Rarara Ya Fitar da Sabuwar Waka, Ya Jajantawa Wadanda Ambaliya Ta Shafa
- Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan ambaliyar ruwan da ta afku
- Kafin kai ziyara Maiduguri, Rarara ya fara rera wakar jaje ga wadanda ambaliyar ruwan ta shafa da ya yiwa taken 'Borno ku yi hakuri'
- A zantawarmu da jarumi a masa'antar Kannywood, Yau Shareef ya bayyana cewa abin da Rarara ya yi ya kyauta domin ya isar da sako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Fitaccen mawakin siyasa daga Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya fitar da sabuwar waka da ya yi wa taken 'Borno ku yi hakuri.'
Rarara ya fitar da wakar ne a matsayin jaje ga dubunnan daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa a Maiduguri ta rutsa da su.
Rarara ya ziyarci jihar Borno
A wani faifan bidiyo da mawakin ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, an ga Rarara tare da wasu jaruman Kannywood a kwale-kwale.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bisa ga dukkan alamu, mawakin na daukar bidiyon wakar ne a tsakiyar wata anguwa da har yanzu ke cike da ruwa, inda A'isha Umaira ke yi masa amshi.
An ce mawakin tare da rakiyar jarumai, da suka hada da Ali Artwork, A'isha Umaira, G Fresh Al'Ameen, Musa Mai Sana'a da kuma mai maganin Al Hikima.
Wani faifan bidiyon na daban a Instagram ya nuna mawakin tare da tawagarsu a tsakiyar dandazon mutanen Maiduguri da tsakiyar dare.
Me Rarara ya ke cewa a wakar?
A cikin sabuwar wakar da ya yi, Rarara ya yi kira ga al'ummar Borno da su yi hakuri domin ambaliyar ruwan daga Allah ne kuma sauki na nan zuwa a gaba.
Mawakin na cewa:
"Matsalar ga ta Boko Haram ba ta shude,
"Ga tabonsu na gobara a garin bai goge ba,
"Kuma ga ambaliyar ruwa ba su shirya ba,
"Ahadin ke nan yadda ya so haka zai yi Tabara gwanin Sarki."
Rara ya ci gaba da cewa:
"Jama'ar Maiduguri kowa na dada kokawa,
"Mata da maza yara sun gaza zaunawa,
"Ciki da wajen kasarmu suna jajantawa,
Wayyo wayyo ni sai na ga kananan yara babu kudin kwaki."
Kalli bidiyon a nan kasa:
Wakar jaje: 'Rarara ya kyauta'
A zantawarmu da jarumin fina finai, Ya'u Shareef ya bayyana cewa abin da mawaki Rarara ya yi ya kyauta, kuma wannan na nuni da cewa ya damu da abin da ke faruwa a kasar.
Ya'u Shareef ya ce wadanda ke zagin Rarara saboda ya yi wakar jaje sun manta da wakar da Aminu Bagwai ya yi lokacin da jirgin ruwa ya kife da wasu a garin Bagwai.
Jarumin ya ce sau tari ana yin amfani da waka wajen isarwa miliyoyin mutane wani sako da babu wata hanyar sadarwa da za ta iya isar da shi ga jama'a.
Gwamnoni sun tallafawa Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla gwamnatocin jihohi tara ne suka tallafawa jihar Borno bayan ambaliyar ruwa ta yi barna a birnin Maiduguri.
An rahoto cewa gwamnatocin jihohin sun tarawa Borno tallafin Naira biliyan 1.1 yayin da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya hada mata da jiragen ruwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng