Daga Karshe: Rarara ya rera wa masoya Buhari wakar da suka biya kudi ya rera

Daga Karshe: Rarara ya rera wa masoya Buhari wakar da suka biya kudi ya rera

  • Mawaki Rarara ya cika alkawari, ya saki sabuwar wakar shugaba Buhari da ya karbi kudi dominta
  • Rarara a baya ya ce ba zai sake yi wa Buhari waka ba har sai an tura masa kudi don tabbatar da kaunar Buhari
  • Masoya Buhari sun yi dandazo don tura N1,000 kuma yau dai kwalliya ta biya kudin sabulu an saki wakar

Shahararren mawakin shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya cika alkawarin da ya dauka na rera wa shugaba Buhari waka, wacce masoya shugaban suka dauki nauyi.

Shekaru kusan biyu da suka gabata Rarara ya bayyana cewa, ba zai sake yiwa shugaba Buhari waka ba har sai masoya Buhari kowa ya tura N1,000 kafin ya rera wata sabuwar wakar Buhari.

Lamarin ya jawo cece-kuce yayin da aka tura masa makudan miliyoyi, kamar yadda wasu majiyoyi suka rahoto, amma bai saki wata waka ba.

Kara karanta wannan

Buhari da hannunsa ya bani lambar waya muna gaisawa amma bai tsinana min komai ba

Daga Karshe: Rarara ya rera wa masoya Buhari wakar da suka tura masa kudi ya rera
Dauda Kahutu Rarara | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: UGC

A halin da ake ciki, Rarara ya ce ya cika alkawari, inda ya buga a shafinsa na Facebook a jiya Lahadi 26 ga watan Satumba cewa ya rera wakar ga Shugaba Buhari.

Da yake sakin wakar, Rarara ya yi rubutu a jikin wani bidiyon sauti cewa:

" ℎ 1 ."

Abin da wakar ke magana akai

A wani bangare na wakar da Legit.ng Hausa ta samo, mun ji cewa, Rarara na magana ne kan ayyukan da shugaba Buhari ya tafka wa 'yan Najeriya.

A cikin wakar, Rarara ya lissafa wasu ayyukan shugaba Buhari, inda yake yaba masa yana kara tabbatar da shugaban a matsayin jigon da ya yi manyan ayyukan.

Martanin wasu mutane a kafar Facebook

Kara karanta wannan

A yunwace jama’a suke, ka yi wani abu kafin su yi wani abu, Dino Melaye ga Shugaba Buhari

Jim kadan bayan sakin wakar, mutane da dama sun yi martani kan wakar da Rarara ya saki. Duba wasu daga ciki:

Sadeeya Sadeeq ya ce:

"Agayawa oga rarara inasan zan fara mashi amshin wakokin shi domin muma muna motar buhari duk da de munaji dukan genaral Asama domin muma bahariyya ta tabamu"

Lawal Ahmad shi kuwa suka ya yi, inda yace:

"Gsky batayi dadi ba a turoman kudina in ba hakaba ban yafeba"

Shamwilu Salihu ya yi martani da cewa:

"Gaskiya nadade Banga shegen kauyen daya rainawa Yan birni wayo ba kamar rarara, Dan kauye, kolo, kazami, wai shine zai karbe muku dubu dubu wai zaiwa buhari Waka, toh me buhari ya tsinana muku musamma ku Yan arewa, yalalata muku tattalin arzikin ku, babu tsaro na rayuka da dukiya, shiyasa kullum Yan kudu suke kallonmu wawaye, wane dan iskane ya isa yace wai subashi kudi zaiyiwa wani shasha Sha Waka, haba jama'a."

Kara karanta wannan

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

Aminu Malam Sokoto yace:

"An Gaisheka Farfesan Waka Dauda RaRa Na Kahutu. Aikin Ka Na Kyau Saidai Adawa. Gaba-Dai Gaba-Dai. Sarkin Waka Na BABA BUHARI Da Sakkwatawa."

Rabiu Badaru yace:

"Duk Wanda yaji Wannan wakar Dole in yanada halin Kara wata 1k din sai ya Kara ba Shugaban Jami ar ma wakan Hausa Alh Dauda Kahutu Rararan Allah ya qara basira"

Buhari da hannunsa ya bani lambar waya muna gaisawa amma bai tsinanamin komai ba

A bangare guda, wani dan Najeriya ya bayyana kokensa ga shugaba Buhari, inda ya ce shugaban bai masa komai duk da cewa ya sha wahala wajen yakin neman zaben shugaban kasa.

Mutumin, wanda ya bayyana sunansa da Badamasi Sima Memai ya bayyana a cikin wani bidiyon da ya yi yawo a kafar sada zumunta ta Facebook a shafin Nasara Radio 98.5 FM, inda ya ke nuna rashin jin dadinsa da halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Ina alfahari da ayyukanka: Buhari ya taya Okorocha murnar cika shekaru 59

Badamasi ya bayyana irin wahalar da ya sha da shi da ire-irensa basu kaunar shugaba Buhari lokacin yakin neman zabe, inda ya ce sun jure watsa musu ruwan zafi da aka yi amma basu saduda akan shugaban ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.