Rigima Ta Kaure Tsakanin Fitacciyar Jarumar Kannywood da Mabiyanta a Soshiyal Midiya

Rigima Ta Kaure Tsakanin Fitacciyar Jarumar Kannywood da Mabiyanta a Soshiyal Midiya

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi ta harzuka da irin yadda wasu mabiyanta ke fada mata bakaken maganganu a intanet
  • Bayan sun kaita makura, jarumar ta ware lokaci inda ta rika mayar masu da martani dai dai bakar maganar da suka yi mata
  • Ba wannan ne karon farko da jaruma Nafisa ke cin karo da suka daga ma'abota soshiyal midiya ba kan irin tsarin salon rayuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Da alama dai hakurin jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi kan masu zaginta a soshiyal midiya ya fara karewa, domin ta fara mayar da martani.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi fice a masana'antar Kannywood, musamman yadda salon gudanar da rayuwarta ya sha bamban da sauran matan masana'antar.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an aikawa malamai N16m domin hana matasa zanga-zanga a Arewa?

Nafisa Abdullahi ta yi martani ga mabiyanta da ke zaginta a soshiyal midiya
An yi musayar yawu tsakanin jaruma Nafisa Abdullahi da mabiyanta a soshiyal midiya. Hoto: @NafisatOfficial
Asali: Twitter

An caccaki Nafisa kan busa hayaki

A baya bayan nan aka ga wani bidiyon Nafisa Abdullahi tana zuka da busar da hayaki, wanda wasu ken tunanin ko wiwi ce, bidiyon da ya jawo cece kuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'abota soshiyal midiya sun caccaki jarumar kan fitar wannan bidiyon, kamar yadda muka tattaro ra'ayin wasu a kasa:

@dankura20

"Barta ta sha wiwi abin ta. Nata ne ya fito fili. Abin da wasu matan ke sha ko ni kai na ba zai dauka ba"

@Babagasa1

"Kasan fa masana sun yi rubuce rubuce a kan cewa rashin aure ma fa na kawo irin haka."

Kalli bidiyon a kasa:

Nafisa ta je kallon wasan Chris Brown

Ba iya bidiyon busa hayakin jarumar ne kadai abin da ya jawo cece kuce ba, har da ziyarar wajen da fitaccen mawaki Chris Brown ke wasa a kasar waje da Nafisa ta yi.

Kara karanta wannan

Ndume ya magantu kan barin APC zuwa PDP bayan dakatar da shi daga mukaminsa

Jarumar ta wallafa bidiyonta a wurin da mawakin ke gabatar da taro, lamarin da mabiyanta suka rika nusar da ita cewa ta yi hattara da salon irin rayuwar da take yi.

Sai dai Nafisa Abdullahi ba ta kai zuciya nesa a wannan karon ba, inda ta ware lokaci, ta rika mayar da martani ga dukkanin wadanda ke aikata ba.

Nafisa ta yi wa mabiyanta martani a X

@ii_khaleedor

"Ki na wuta! Amma za ki iya shiga wuta."

Nafisa Abdullahi ta yi masa martani da cewa: "Kai ma za ka iya shiga."

@BujiMustapha

"Aunty Allah ya sa ba giya bane"

Nafisa Abdullahi ta ba shi amsa da cewa: "Dan uwa giya din ce."

@banney___

"Aringa sa hula ko dankwali da Allah, nafisatu."

Nafisa Abdullahi ta ba shi amsa da cewa: "Kwarai zan saka, amma lokacin da na ga dama."

Kalli bidiyon a kasa:

"Ba ku san komai ba" - Nafisa

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Daga bisani, jarumar ta kuma saki wani rubutu, inda take bayyana cewa mabiyanta ba za su taba gane inda ta dosa ba sai idan ita ce ta nuna masu, a hakan ma ba su gane ba.

Jarumar ta ce:

"Mutanen shoshiyal midiya suna tunanin sun san ka saboda abubuwan da kake nuna musu, Sai dai kuna ganin abin da na nuna maku ne kawai.
"Idan ban nuna ba, ba ku za ku san komai ba! Idan na nuna maku din ma ba ku san komai ba."

Hotunan Nafisa Abdullahi sun tada hazo

A wani labarin, mun ruwaito cewa jama'a sun tofa albarkacin bakinsu bayan bayyanar sababbin hotunan Nafisa Abdullahi a dandalin soshiyal midiya.

Nafisa na cikin jerin manyan jaruman Kannywood da suka halarci bikin taya Ali Nuhu murnar samun mukami a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda aka yi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.