Jaruma Nafisa Abdullahi ta fitar da sabbin zafafan hotuna cikin sabon launi
Fitacciyar jarumar wasan fina-finan Hausa, Nafisa Abullahi, ta fitar da wasu zafafan hotuna masu kayatar wa cikin sabon launin da ta ce ita kanta yana kayatar da ita.
A hotunan da ta fitar a shafinta na sada zumunta, Nafisa ta rubuta, cikin harshen turanci, cewar; "yanzu na samu wani launi da nake matukar.....(launin makuba)".
Hotunan jaruman sun ja hankalin masoya da magoya bayanta, wadanda suka bayyana yadda ta burge su a cikin sabon launin makuba da ta ce tana so.
A cikin makon jiya ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kaca-kaca da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin cewa komai a kan kashe-kashen da ake yi a wasu kauyukan jihohin Zamfara.
DUBA WANNAN: Uwa ba ta fi uwa ba, ni ma zan zagi mahaifiyarka tunda ka zagi tawa - Adam Zango ya shiga rigima da fitaccen jarumin Kannywood
Jarumar ta soki shugaba Buhari a bisa maganan da ya yi a kan kisan wani matashi, Kolade Johnson da wasu 'yan sanda biyu suka yi a Legas amma bai ce uffan ba a kan kisan kiyashin da 'yan bindiga su ke yiwa al'umma a Zamfara ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng