‘Dan Wasa Zai Mikawa Gwamna Abba Rikon Yaransa 2 Saboda Dakatar da Shi Daga Fim a Kano
- Abdul Haseer (Malam Ali a shirin Kwana Casa’in) ya fitar da sakon bidiyo na musamman zuwa ga gwamnan jihar Kano
- A bidiyon, ‘dan wasan ya ce hukumar tace fina-finai ta dakatar da shi ba tare da adalci ba, yanzu bai da hanyar neman abinci
- Ganin halin da ya shiga, tauraron ya sha alwashin daukar yaransa zuwa wajen Abba Kabir Yusuf domin a kula da dawainiyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano – Abdul Haseer wanda ya shahara da suna Malam Ali a shirin Kwana casa’in, ya koka game da dakatar da shi da aka yi daga harkar fim.
A bidiyon da Abdul Haseer ya fitar a dandalin sada zumunta wanda mu ka ci karo da shi a Twitter, ya aikawa Gwamna Abba Kabir Yusuf sako.
Malam Ali ya soki hukuncin da aka yanke
Jarumin ya sanar da Mai girma Abba Kabir Yusuf cewa an yi masa hukunci wanda a cewarsa, ya saba ka’ida yana kokarin jan hankalin mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdul Haseer ya ce burinsa shi ne ganin ya wayar da kan matasa musamman mata, a karshe sai hukumar tace fina-finai ta zarge shi da batsa.
Jawabin Malam Ali zuwa ga Gwamna Abba
"Babu wani mahaluki mai hankali wanda zai zo ya ga ‘yarsa, matarsa, kanwarsa ko kuma yayarsa suna rawan zubar da mutunci, suna sa damammun kaya a shafukan sada zumunta, musamman kafa ta Tik Tok.
Ya Mai girma Gwamnan jihar Kano, wannan dalili ya sa na ke amfani da hanyoyi dabam-dabam wajen ganin cewa na jawo hankalin matasanmu da ni kai na, musamman ‘ya ‘ya mata da yakana, alkunya da kamun kai.
Ya Mai girma Gwamnan jihar Kano, ina tura sakonnina ba tare da cin mutunci ga addina ko jihar Kano. A matsayinka na uba a jihar Kano, ina so in yi amfani da wannan damar in fada maka cewa an dakatar da ni daga shirya fina-finai a masana’antar Kannywood na shekara biyu ba tare da ka’ida ba."
- Abdul Saheer
Me Malam Ali yake nema wajen Gwamna Abba?
A lolacin da gwmanatin Abba ta ke kokarin samar da ayyukan yi da ilmi, tauraron ya ce an yanke masa danyen hukunci ba tare da yin adalci ba.
Ganin ana yi masa zaton shi shugaba ne mai adalci da tausayi, Abdul Saheer ya fadawa Abba Gida Gida cewa an karbe masa hanyar neman abinci.
A matsayinsa na ‘dan Kano da ya rasa aikin yi, tauraron ya ce zai kai ‘ya ‘yansa wajen gwamna domin a cigaba da dawainiyar cinsu da shan su.
Na tsawon shekarun nan biyu, ‘dan wasan ya nuna bai da yadda zai iya tufatar kuma ya kai ‘ya ‘yansa makaranta, sai gwamnati ta taimaka masa.
Menene dalilin dakatar da Malam Ali?
A baya labari ya zo cewa tauraron zai yi shekaru 2 bai fito a wasan kwaikwayo a Kano ba saboda matakin da Hukumar tace fina-finai ta dauka.
Hukumar ta zargi jarumin da ya yi suna a dandalin sada zumunta na Tik Tok da wallafa bidiyon batsa, da kin amsa gayyatar da aka yi masa.
Asali: Legit.ng