Manyan Jaruman Kannywood Mata, Tsoffi Da Na Yanzu Sun Hadu A Wajen Liyafar Kungiyarsu, Sun Girgije A Bidiyo
- Kungiyar AFAKA ta jaruman masana'antar Kannywood mata sun gudanar da wani gagarumin taro
- Shugabar kungiyar, Rashida Adamu Albadullahi Maisa'a, ta ce daga yanzu a shirye suke suma a dama da su a dukkan bangarori kama daga talluka da harkokin siyasa
- Manyan jarumai mata, tsoffi da na yanzu duk sun halarci taron inda suka sha rawansu suka girgije
Kungiyar jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood mata mai suna AFAKA ta gudanar da wata kasaitacciyar liyafa kara dankon zumunci.
Taron ya samu halartan manyan jaruman fim mata na da da yanzu, inda suka sha rawa suka girgije.
A wata wallafa da shugabar kungiyar, Ambasador Rashida Adamu Albadullahi Maisa'a ta yi a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa daga yanzu suna za a dunga damawa da su a kowani bangare.
Rashida Maisa’a ta kuma jaddada cewa za su dunga karbar talluka da kamfen din siyasa da ma duk wata harka na alkhairi da za ta biyo hanyarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin jaruman da suka hallara akwai Samira Ahmad, Mansurah Isa, Hadizan Saima, Asma’u Sani, Aina’u Ade, Halima Atete, Zahra’u Shata, Hadiza Kabara, Muhibbat AbdulSalam.
Sauran sune Sadiya Gyale, Fauziyya mai kyau, Jamila Gandarai, Sadiya Rarara, Sadiya Haruna da sauransu.
Hakazalika akwai wasu jarumar maza da suka hallara kamar su Umar Gombe, Muhammad Sharukan da sauransu.
Kalli bidiyoyin taron a kasa:
Gwamnatin Nan Ta Gaza Mana, In Ji Jaruma Maryam Booth Kan Bidiyon Dukan Fasinjojin Kaduna-Abuja
A wani labari na daban, fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Booth ta bi sahun takwarorinta wajen yin tir da sabon bidiyon da yan ta’adda suka saki inda suke jibgan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.
Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua
Maryam Booth a wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram ta bayyana cewa lallai wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gazawa al’ummanta.
Jarumar ta bayyana hakan ne a rubuce a kasan bidiyon da miyagun suka saki inda suke ta dukan fasinjojin wadanda suka yi garkuwa da su tun a ranar 28 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng