Ina bukatar Mijin aure cikin gaggawa, Jaruma a masana'antar Fina-Finai ta cire kunya

Ina bukatar Mijin aure cikin gaggawa, Jaruma a masana'antar Fina-Finai ta cire kunya

  • Jaruma a masana'antar shirya Fina-Finai, Eucharia Anunobi, ta sanar da duniya halin da take ciki na bukatar mijin aure
  • Yayin zantawa da kafar watsa labarai, Jarumar ta ce tana son mijin da zata aura ya gaggauta bayyana kuma ya zama cikakken namiji, kyakkyawa
  • A cewarta ta ƙosa ta samu wanda zai amince ya sanya mata zoben aure a yatsan hannunta

Fitacciyar Jaruma a masana'antar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Eucharia Anunobi, ta ce tana binciken mijin da ya shirya su yi aure ba tare da ɓata lokaci ba.

A wata hira da kafar BBC Igbo, Anunobi, ta bayyana cewa tana tsananin bukatar samun mutumin da zai sa mata zoben aure a hannunta nan ba da jimawa ba.

Jarumar wacce ta kai kimanin shekara 56 a duniya ta ce tana fatan ta auri mutumin da ya cika ya haɗa duk abin da ake bukata na zama Magidanci.

Kara karanta wannan

“Na Rasa Sukuni”: Dan Najeriya Ya Koka a Bidiyo, Ya ce Matar Da Ya Aura Ya Kai Turai Tana Sharholiya Da Maza

Jaruma Eucharia Anunobi.
Ina bukatar Mijin aure cikin gaggawa, Jaruma a masana'antar Fina-Finai ta cire kunya Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto jarumar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dan Allah ina amfani da wannan damar na sanar da duniya cewa ina masifar son aure cikin gaggawa. Wani babban mutum cikakke ya fito ya sanya mun zoben aure a hannu na."
"Abubuwan da nake son mijin da zan aura ya haɗa sune ya zama mai tsoron Allah kuma kyakkyawa, wajibi ya zama cikakke wanda ya haɗa duk wani abu da mutum ke zama namiji."
"Zaɓi na kenan kuma abin da nake bukata kenan wajibi ne mijin da zan aura ya zama cikakken namiji."

Ko tana soyayya da wani a Nollywood?

Rahoto ya nuna cewa Jarumar ta na soyayya da wani abokin aikinta a Nollywood matashi ɗan shekara 27, Lucky Oparah, lamarin da ta musanta.

Haifaffiyar Owerri jihar Imo, Jaruma Anunobi bayan gama Sakandire, ta zarce zuwa makarantar fasaha IMF inda ta samu shaidar kammala karatun Diploma a fannin aikin jarida.

Kara karanta wannan

Budurwa ta bi Saurayi a Wurin Biki ta Tashe shi, Zai Aureta Bayan Shekaru Uku a Bidiyo

Tauraruwarta ta fara haskawa ne a shekarar 1994 lokacin da ta fito a wani shiri mai dogon zango mai suna 'Glamour Girls'.

A wani labarin kuma Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Wasu daga cikin Jaruman Kannywood da tauraruwarsu ke haskawa sun bayyana tsayawa takarar siyasa a zaɓen 2023.

Mun tattaro muku waɗan nan jaruman da suka nuna sha'awar ba da gudummuwarsu a ɓangaren shugabancin al'umma a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel